logo

HAUSA

Yadda Amurka ke siyasantar da batun COVID-19

2020-04-29 21:59:59 CRI

Yanzu haka, babban abokin gaban daukcin bil-Adama, shi ne COVID-19, Sai dai yayin da kasashen duniya ciki har da kasar Sin ke kokarin taimakawa kasashen duniya da wannan cuta ke ci gaba da addaba ganin bayanta, a hannu guda kuma wasu 'yan siyasar Amurka sun kasa mayar da hankali kan yadda cutar ke tsananin yaduwa a sassan kasar, sabanin yadda mahukuntan kasar Sin ke ba da muhimmanci ga rayukan al'ummunta, da ma na 'yan kasashen waje dake cikin kasar, ta hanyar daukar matakan da suka dace cikin gaggawa, inda suka tura likitoci da nas nas sama da dubu 42 zuwa ga lardin Hubei, a sa'i daya kuma, al'ummun kasar da yawansu ya kai biliyan 1 da miliyan 400 sun killace kansu a cikin gida bisa radin kansu, matakin da ya kai ga sake bude birnin Wuhan a halin yanzu.

A karshen watan Maris, mujallar kimiya ta "Science" ta fitar da wani sakamakon nazari, inda aka nuna cewa, a cikin farkon kwanaki 50 bayan barkewar cutar, an rufe birnin Wuhan, matakin da ya hana mutane sama da dubu 700 a sassa daban daban na kasar waje da birnin kamuwa da cutar, a sanadin haka, adadin mutanen da aka killace da za su kamu da cutar a kasar Sin ya ragu da kaso 96 bisa dari. Wannan shi ne dalilin da ya sa kasar Sin ta rage mutanen da suka mutu sakamakon cutar fiye da kima.

Yayin da kasar Sin ta yi nasarar ganin bayan wannan annoba, har ma ta ke raba fasahohi da ma tura kayayyaki da jami'an kiwon lafiya zuwa kasashen duniya daban-daban, ita kuma gwamnatin Amurka ba ta dauki matakan da suka dace ba a kan lokaci yayin da take dakile annobar, har tana dora laifi kan wasu, inda ta ke ci gaba da hada annobar da batun siyasa, da ci gaba da siyasantar da batun , matakin da ka iya cusa Amurkawa cikin kunci da wahala. Amma masu iya Magana na cewa, mai daki shi ya sa inda yake masa yoyo. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)