logo

HAUSA

Garzali Gali: Ina jin dadin karatu a China

2020-04-29 08:56:10 CRI

Garzali Gali: Ina jin dadin karatu a China

A kwanan nan, Murtala Zhang ya zanta da wani dalibi dan jihar Kanon Najeriya, mai suna Garzali Gali, wanda a yanzu haka yake karatun digiri na farko a fannin gine-gine, a jami'ar kimiyya da fasaha ta Changsha dake lardin Hunan na kasar Sin, wato Changsha University of Science and Technology.

Garzali Galin ya ce, yana jin dadin karatu a kasar Sin, kuma burinsa shi ne yin amfani da ilimin da ya samu a kasar wajen bautawa kasarsa Najeriya. Kana, Garzali Gali ya yi kira ga baki 'yan kasashen waje dake zaune a Sin, da su rika bin doka da oda a kasar, musamman a lokacin da ake himmatuwa wajen ganin bayan cutar numfashi ta COVID-19.(Murtala Zhang)