Peng Jing, ma'aikaciyar wata unguwa: in babu hadin gwiwa, ba za a iya dakile yaduwar cutar COVID-19 da saurin haka ba
2020-04-28 13:23:18 CRI
Yanzu duk duniya na fama da cutar COVID-19, ciki har da kasar Sin. Yayin da ake yaki da cutar a kasar, unguwoyin zama na taka muhimmiyar rawa, ma'aikatan unguwoyin kuwa na bayar da babbar gudummawa a cikin wannan yakin musamman. A cikin shirinmu na yau, bari in gabatar muku labarin Madam Peng Jing, wata ma'aikaciyar unguwar zama da ke birnin Wuhan. Yayin da ake fama da cutar COVID-19, ita da mazauna unguwar fiye da dubu 10 sun hada gwiwa sosai wajen kare kansu daga cutar da ma kokarin samun nasara a kan cutar.
Madam Peng Jing, shugaba ce mai kula da ayyukan unguwar Shuianxingcheng da ke birnin Wuhan. Tun bayan bullar cutar COVID-19 mai tsanani, yadda za a kokarta don dakile yaduwar cutar da ma tabbatar da lafiyar mazauna unguwar fiye da dubu 10 ya zama aikin da ke gaban komai a gare ta. Ko da yake ana maido da zaman al'umma sannu a hankali yanzu, amma aikin kandagarki da takaita yaduwar cutar COVID-19 shi ne wanda Peng Jing ta fi mai da hankalinta a kai. "har zuwa yanzu ba mu iya kawar da hankalinmu kan aikin dakile cutar ba. Hakika dai, gare mu, da mazauna unguwar, yanzu dukkanmu mun yi sassauta, don haka akwai bukatar mu gargadesu."
Madam Peng Jing mai shekaru 33 da haihuwa, ta kware wajen aiki da iya magana. Amma ta gaya min cewa, a farkon bullar cutar COVID-19, ita kanta dake da gogewar aiki har na tsawon shekaru 11, hankalinta ta tashi, kuma ba ta san abun da ya kamata ta yi ba.
"A wancan lokaci, ko da yashe ina amsa wayoyin da mazauna unguwar suke buga min domin neman shiga asibiti da ma ganin likita sabo da rashin lafiyar, wayoyin sun zarce 100 a ko wace rana. Na kan yi barci sa'o'i hudu ko biyar kawai a ko wace rana. Amma na fahimce su sosai, babu wanda ba zai ji tsoron irin wannan annoba mai matukar tsanani ba." Daga baya kuma, an fara rufe unguwanni a birnin Wuhan don hana shige da fice. Ban da aikin rigakafi da takaita yaduwar cutar, mu ma'aikatan unguwar muna da kula da ayyukan saya wa mazauna unguwar kayayyakin masarufi da aika musu kayayyakin.
Kasancewar gidaje fiye da 4300 a unguwar Shuianxingcheng, da ma ma'akatan unguwar 11 kadai, ya dami Peng Jing sosai. Domin warware matsalar karancin ma'aikata, ta fara daukar masu aikin sa kai daga cikin mazauna unguwar. Abin da ya wuce zatonta shi ne, aikin ya samu goyon baya daga dimbin mutane.
"Na fada wa mazauna unguwarmu cewa, : idan mun dakile yaduwar cutar COVID-19 a unguwarmu, sauran mazauna birninmu sun dakile yaduwar cutar a unguwoyinsu, to za mu iya samun nasara kan cutar a duk garinmu. Bayan na bayar da sanarwar da tsakar rana, to ya zuwa karfe 9 na daren ranar kuwa, masu aikin sa kai 96 sun bayyana aniyarsu ta taimaka mun wajen kula da unguwarmu. Lallai abun da ya burge ni sosai." Bayan samun isassun ma'aikata, an fara gudanar da ayyuka daban daban na kula da unguwar yadda ya kamata. Domin gudanar da aikin dakile yaduwar cutar a unguwarta yadda ya kamata, Peng Jing ta dauki matakai daban daban. Kamar ita da sauran ma'aikata su kan sabunta sanarwoyi a ko wace rana domin mazauna wurin su samu labarai a kan lokaci. Sun kuma sanar da aikin fesa kwayoyin cuta ta manjahar Wechat, wadda kusan kowa na amfani da ita. Haka kuma sun watsa labarai kan ilmin kandagarki da dakile yaduwar cutar ta rediyo domin gargadin mazauna wurin wajen kara kare kansu. A hankali a hankali, Peng Jing ta gano cewa, mazaunan sun fara dora muhimmanci kan cutar da ma kwantar da hankalinsu, a maimakon jin tsoro. "Cutar ta bulla kwatsam, kowa na jin tsoro sosai domin ba a taba ganin irinta ba. Amma daga baya, an fara samun wata hanyar da ta dace wajen tinkarar matsalar. Yanzu mazauna unguwarmu hankalinsu ya kwanta, ba sa jin haushi da fargaba kamar a lokacin farko."
Abin da ya faranta ran Peng Jing shi ne, bayan da suka yi kokarin aikin har na tsawon wasu lokuta, sai mazauna unguwar suka aminta da su sosai.
"ma'aikatan unguwarmu da ma masu aikin sa kai su kan fara aiki da karfe 8 na safe har zuwa karfe goma na dare, lallai sun sha wahala sosai domin kokarin kiyaye lafiyar ko wanen mazauni." Sakamakon cutar COVID-19 ta samu sauki sosai a birnin Wuhan, don haka an sake bude birnin, kuma mazauna wurin sun fara komawa zamansu na yau da kullum. Amma ana bukatar ci gaba da aikin dakile yaduwar cutar a unguwanni. A ganin Peng Jing, yaki da cutar na bukatar kowa ya kame kansa, kuma a hada gwiwa sosai. "Da farko dai, ya kamata kowa ya kame kansa, a bi doka a daina fita waje, don magance haddasa matsala ga zaman al'umma. Ban da wannan kuma, ya kamata kowa ya ba da gudummawa bisa karfinsa. Idan babu hadin kan mutane, da ma taimakon da aka ba mu daga sassa daban daban, to da ba za mu iya dakile cutar da sauri haka ba." Yanzu Peng Jing na lura da sabon labari kan cutar na duk duniya. A matsayinta ta wadda ke ganam ma idanunta yanayin cutar, tana fatan za a iya ganin bayanta cikin hanzari. "da farko dai, ina fatan kowa na iya kula da gidansa sosai. Hakan zai taimaka wajen ganin kyautatar duk kasa har ma da duniya. Ban da wannan kuma, ina fatan za a iya kawo karshen cutar da wuri. Na fadi hakan ne bisa sahihanci, ganin yadda na taba fama da cutar a inda cutar ta taba fin kamari."
Busasshiyyar taliya ta Madam Zhao wani shaharrren dakin cin abincin safe ne a birnin Wuhan. A lokacin da ake iya gudanar da aiki yadda ya kamata, tsawon jerin gwanon masu zuwa sayen abinci ya kai goman mitoci. Sakamakon bullar cutar COVID-19, an rufe wannan dakin cin abinci har na tsawon watanni fiye da biyu. Amma yanzu an sake bude kofarsa.
Labarin sake bude dakin cin abincin safe na Busasshiyyar taliya na Madam Zhao, ya jawo hankalin mazauna birnin Wuhan masu dimbin yawa. A wajen dakin cin abincin, ana iya ganin cewa, an ajiye wasu taburori, masu ba da hidima ma sun kunshe abinci bisa bukatun masu sayayya, sa'an nan sun ajiye su a kan tebur don masu sayayye su dauka da kansu. Babu mu'amala da tuntuba ko kadan a tsakanin masu ba da hidima da masu sayayya. Madam Zhao Youzhi mai shekaru 62 da haihuwa, ita ce mamallakiyar dakin cin abincin. Da take tunatar da masu sayayya kan kiyaye tazarar da ke tsakanin kowa da kowa, da take kunshe abincin don rage yawan lokacin da ake jira, ta bayyana cewa "yanzu mun tashi da wuri, sabo da muna bukatar lokacin fesa kwayoyin cuta a ko ina, da auna zafin jikin masu ba da hidima domin gudanar da aikin rigakafin cutar yadda ya kamata. A halin yanzu, muna bukatar zuwa dakin sayar da abincin da wuri da wajen sa'a daya ko biyu in an kwatanta da na da."
A cikin shekaru fiye da 20 da suka gabata, Madam Zhao na bin ka'idar rufe dakinta na sayar da abincin a jajibirin sabuwar shekara, da ma sake bude shi a ranar 8 ga watan farko na sabuwar shekarar. Madam Zhao Youzhi ta bayyana cikin alfaharin cewar, ta cancanci yabon da aka yi wa dakin na ba wa mutane damar jin dadin cin busasshiyar taliya a ko wace rana. Amma a wannan shekarar bana, ba ta bude dakinta a ranar 8 ga watan farko na sabuwar shekara ba.
"Bubu shakka muna gaggawa wajen sake bude dakin sayar da abincin. Sabo da ko wane ma'aikaci ba shi da albashi in ba ya da aikin yi. Ban da wannan kuma na riga na biya kudin hayar dakin, mun sha asara sosai a cikin watannin biyu da suka gabata. Amma mun fahimci manufar gwamnati, an yi hakan ne don kare mu daga cutar. Yanzu mun sake maido da aikinmu, ya kamata mu dauki matakan rikakafi sosai don tabbatar da lafiyar ma'aikatanmu." Abin da ya kwantar da hankalin Madam Zhao shi ne, akwai wayoyi masu dimbin yawa da aka buga mata don tambyar lokacin sake bude dakin cin abincin, lallai ba a manta da dakinta ba. "ba mu bude kofarmu bayan ranar 8 ga watan farko na bana ba, amma akwai mutanen da su kan buga mun waya a ko wace rana, daga guda 8 ko 9 a lokacin farko har zuwa kimanin 50 bayan wata guda, domin tambayar ko za mu iya aika musu abincin, sai mun yi musu bayani sosai. Lallai mutane na son cin abincinmu." A lokacin fama da cutar COVID-19, Zhao Youzhi na lura da labarai a ko wace rana. Da ta ga labarin kan cewa, yawan sabbin masu dauke da cutar ya ragu kasa da goma, ta gano cewa, za a iya sake farfado da ayyuka ba da dadewa ba. Don haka, nan da nan bayan fitar da manufar farfado da aiki, Madam Zhao ta gabatar da bukatarta ba tare da bata lokaci ba. "Da na samu labarin cwea, gwamnati ta amince da wasu kamfanoni su dawo da ayyukansu, nan da nan na rubuta takardar roko. Lallai gwamnatin ta mara mana baya sosai, bayan kwanaki biyu kadai, aka amince da rokona. Watakila sabo da dakin cin abincin namu ya shahara a nan. Bayan mun samu amincewa, sai muka fara aikin shiri." "An kulle mu a gida har na tsawon kwanaki da yawa, don haka muna farin ciki sosai da iya fita waje don cin kayan marmari, ganin yadda ake iya samun yawan nau'o'in kayayyakin marmari a nan birnin Wuhan." "Iyayenmu sun taba cin taliyar nan, sun ce akwai dandano sosai. Don haka na zo nan don saya musu taliyar."
Zhao Youzhi ba ta damu ko kadan kan harkokin kasuwacinta ba.
"ina da imani kan sake bude kofar kantina, sabo da karbuwarta daga mazauna wurin. Na sani, tabbas akwai mutane da yawa da za su zo don cin taliya. Cikin tsawon lokaci ba a ci taliyar ba, don haka za su gamsu sosai da zuwa kantina don cin abincin." Farashin busasshiyar taliya ya kai Yuan 9 ga babban kwano, kuma Yuan 6 ga karamin kwano. Ko da yake farashin kayayyakin hada taliyar ya karu bayan sake bude kantin, amma Zhao Youzhi ta yanke shararar cewa, ba za ta kara farashin taliyar ba. "Ba zan kara farashin taliyarmu ba. sabo da idan na kara farashin, masu sayayya ba za su ji dadi ba, kuma martabar da aka nuna mun za ta baci. Yanzu lokacin musamman ne, ko da ba mu samu riba da yawa ba, ba damuwa."
Ban da wannan kuma, Madam Zhao na tunanin cewa, bayan ganin bayan cutar COVID-19, za ta habaka girman kantinta domin masu sayayya su ji dadin cin abinci a wurin.
"Sabo da kayayyakinmu na da inganci a ko da yaushe, don haka muna da imani sosai yanzu. Hakata ta cimma ruwa."(Kande Gao)