logo

HAUSA

Dan Wasan motsa jiki dan gudun hijira Lokoro ya yi kira da a maida hankali da aiki tukuru gabanin gasar Tokyo ta 2021

2020-04-23 15:14:35 CRI

Dan Wasan motsa jiki dan gudun hijira Paulo Amotun Lokoro, ya yi kira ga tawagar 'yan wasan sa da su maida hankali, su kuma yi aiki tukuru wajen samun horo, gabanin gasar Olympic ta birnin Tokyo da ke tafe cikin shekarar 2021. Paulo Amotun Lokoro, wanda ke cikin 'yan wasan tsare masu wakiltar 'yan wasa 'yan gudun hijira, ya ja hankalin takwarorin sa da su kauracewa buga wasan kwallon kafa ko kwallon Kwando, yayin da suke zaune a sansanin Kakuma, don gujewa jin rauni. Lokoro, wanda ya shiga gasar Olympics ta birnin Rio, ya ce tawagar su za ta shawo kan kalubalen zama wuri daya da suke fuskanta, a sansanin 'yan gudun hijira na Kakuma dake Arewacin Kenya, nan gaba kuma suna fatan komawa gasanni, gabanin gasar Olympics din ta Tokyo da aka dage zuwa shekarar 2021. Ya ce "Duk wata nasara tana da nasaba ne da irin shirin da aka yiwa gasar ta Olympics, amma yanzu an dage gasar. Hakan zai yi amfani ta wata fuskar, domin zai ba mu karin lokaci na fadada shirin mu. Yanzu dole na yi shiri sosai domin shekarar mai zuwa. A ra'ayi na, ina fatan zuwa gasar Tokyo dake tafe". Daga nan sai ya ja hankalin takwarorin sa da kada su daina yin horo, kuma su kaucewa shiga wasu wasanni da ka iya sa su jin ciwo. Paulo Amotun Lokoro ya kara da cewa, "Mun fada musu kada su rika shiga wasanni irin su kwallon kafa a sansanin da suke domin kaucewa jin ciwo. Don haka yanzu wasanni marasa hadari kadai suke yi, ba za su bar jikin su ya yi nauyi ba," "Mu 'yan gudun hijira ne, Ba ma yin kuka. Dole mu zamo cike da kwarin gwiwa. Dole mu jira damar mu." Lokoro dai ya shiga gudun mita 1,500 a gasar birnin Rio, kuma dan asalin kasar Sudan ta kudu ne, wanda kuma a yanzu ke zaune a sansanin 'yan gudun hijira dake birnin Nairobi, karkashin kulawar gidauniyar Tegla Loroupe. Lokoro na fatan himmar su wajen samun horo, za ta ba su damar kafa tarihi mai ma'ana, sama da wanda tawagar ta cimma yayin gasar Olympic na birnin Rio na shekarar 2016. Loroupe dai ita ce babbar jagorar 'yan wasan tsere 'yan gudun hijira da suka shiga gasar Olympic ta birnin Rio a shekarar 2016. Ta kuma bayyana kyakkyawan fatan ta, na ganin daukacin 'yan wasan ta sun cimma nasara, tare da nunawa duniya kwazon su a wannan fage. A baya dai Lokoro, makiyayi ne a kasar Sudan ta Kudu, ya kuma shiga gasar Rio ajin gudun mita 1,500, a matsayin daya daga 'yan tawagar wasa, ajin 'yan gudun hijira, mai dauke da 'yan wasan da tashe tashen hankula suka raba da kasashen su na asali. Da taimakon hukumar wasannin motsa jiki ta duniya, tawagar ta su ta fitar da jerin 'yan wasa da suka wakilce ta, a gasar gudun karbar sanda ta duniya, da gasannin kasa da kasa ta wasannin motsa jiki a shekarun 2017 da 2019, da gasar gudun yada kanin wani ta "Marathon" ajin rabin zango da ta gudana a shekarar 2018, da gasar kewaya sassan kasashen duniya ta kasa da kasa a shekarar 2019. Duk kuwa da cewa ya sake dawowa mafarin shigar sa gasar ta Olympic, wato sansanin Kakuma na 'yan gudun hijira, Lokoro ya ce yana ci gaba da tattaunawa da Loroupe. Ita ma a nata tsokaci game da wannan batu, jagorar gidauniyar Tegla Loroupe ta ce "'Yan wasan na maida hankali, suna zaune tare, suna samun horo tare, suna cin abinci tare suna kuma zuwa makaranta tare. Don haka cutar coronavirus ma ba za ta karya lagon su na fatan cimma nasara ba. Ko shakka ba bu za su yi nasara." Rugani da Matuidi sun farfado daga cutar COVID-19 Nan da dan lokaci 'yan wasan kwallon kafa na kungiyar Juventus mai buga gasar kwararru ta Italiya wato Serie A, Daniele Rugani da kuma Blaise Matuidi za su kammala zaman killacewa da suke yi, bayan da a baya aka tabbatar sun harbu da cutar COVID-19. An ce an yiwa 'yan wasan gwaji a karo na biyu wanda ya tabbatar a yanzu ba sa sauke da cutar. Rugani shi ne dan wasan dake buga Serie A na farko da aka gano yana dauke da wannan cutar a cikin watan da ya gabata, kafin kuma a gano cewa abokan wasan sa Matuidi da Paulo Dybala su ma sun harbu da cutar. Wata sanarwa da kungiyar su ta fitar ta ce "Daniele Rugani da Blaise Matuidi sun samu gwaji, sun kuma dauki matakan da ake da su, an musu gwaje gwaje na cutar Covid 19. Sanarwar ta kara da cewa, "sakamakon gwajin karshe ya nuna a yanzu ba sa dauke da cutar. 'Yan wasan a yanzu, sun riga sun warke, don haka ba sa bukatar ci gaba da killace kai a gida." Rahotanni sun kuma bayyana cewa, shi ma Dybala na daf da warkewa baki daya, amma kungiyar ta Juventus ba ta tabbatar da wannan labari ba tukuna. Zidane Ya Ba Wa Madrid Damar Sayo Kante Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinadine Zidane, ya bukaci Real Madrid din data kawo masa dan wasa N'Golo Kante, wanda Chelsea take shirin sayar dashi a kakar wasa mai zuwa Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dai ta shirya sayar da N'Golo Kante idan har kungiyoyin Paris Saint German da Real Madrid za su iya biyan abinda kungiyar zata bukata kamar yadda rahotanni suka bayyana. Zidane ya na fatan Real Madrid ta sayi Kante domin ya dinga taimakawa Casemiro ko kuma ya zama kishiyarsa kamar yadda wasu lokutan yake samun matsala ta jin ciwo ko kuma dakatarwa sai dai kuma Kante ba zai iya zaman benci ba. Kante, dan kasar Faransa, ya koma kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ne a shekara ta 2016 kuma tun bayan komawarsa ya bayyana kansa a duniya a matsayin babban dan wasan tsakiya kuma ya lashe kofin firimiya daya da kofin kalubale da kuma Europa. Sai dai duk da irin kwarewar dan wasan kociyan kungiyar kwallon kafar ta Chelsea, Frank Lampard ya fara tunanin rabuwa da dan wasan mai shekara 29 a duniya saboda yana fatan sayan matasan 'yan wasa masu jini a jiki. Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinadine Zidane, yana fatan ganin ya dauki dan wasan wanda ya buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Leceister City domin ya hada shi da Paul Pogba da Kylian Mbappe, wadanda Real Madrid din take tunanin dauka. Ita ma kungiyar kwallon kafa ta PSG tana bibiyar dan wasan kuma tana ganin idan har Chelsea ta saka dan wasan a kasuwa zata iya biyan abinda ake bukata domin mayar da dan wasan kasar Faransa ya ci gaba da buga wasa. Kawo yanzu dai Kante yana da ragowar kwantiragin shekara uku a kungiyar Chelsea kuma kociyan kungiyar yana son shugabannin Chelsea su bashi kudi domin ya sayi matasan 'yan wasan da zasu karawa kungiyar karfi a kakar wasa mai zuwa Yakamata Aubameyang Ya Bar Arsenal, Cewar Shugaban Hukumar Kwallon Kafan Gabo Shugaban hukumar kwallon kafar kasar Gabon, Pierre Alain Mounguengui, ya bukaci dan kwallon Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang akan ya koma wata kungiya da ke da tsarin samun nasarori domin ya ci gaba da kafa tarihi kafin yayi ritaya. Dan wasan ya yi kan-kan-kan tare da wasu 'yan kwallon a matsayin wadanda suka fi zura kwallaye a gasar firimiyar Ingila a kakar wasan da ta wuce, inda ya ci kwallo 22 tare da Sadio Mane da Mohammad Salah. A kakar wasa mai zuwa ne kwangilarsa za ta kare a Arsenal sai dai har yanzu bai fara Magana da kungiyar ba domin sake sabuwar yarjejeniya amma kuma rahotanni sun bayyana cewa yana son barin kungiyar ne. "A yanzu yana Arsenal, bai ci kowanne kofi ba kuma kowa yasan babban dan wasa ne wanda ya lashe wasanni sannan ya zura kwallaye da dama saboda haka dan wasa kamarsa yana bukatar lashe kofi in ji ,"Pierre Alain Mounguengui Mounguengui ya kara da cewa " Idan Pierre ya samu wata kungiya, gwamma ya kara gaba saboda na fahimci ba zai iya cin kofi ba a inda yake yanzu kuma muna fatan dan wasan kasar mu ya kafa tarihi a duniya." A watan da ya wuce, kocin Arsenal, Mikel Arteta ya ce yanason Aubameyang ya ci gaba da buga wasa a Arsenal kota hallin kaka sai dai abune mai wahala dan wasan wanda ya koma Arsenal a watan Janairun shekara ta 2018 ya ci gaba da zama, ya koma Arsenal daga Borussia Dortmund a kan fan miliyan 56. Arsenal Na Son Daukar Jovic Daga Real Madrid Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta fara neman dan wasan gaba na kungiyar Real Madrid, Luca Jovic, wanda ake ganin kudinsa zai kai fam miliyan 40 idan za'a sayar dashi. Real Madrid ta dauki Luca Jovic ne daga kungiyar kwallon kafa ta Frankfurt dake kasar Jamus a kakar wasan data gabata sai dai tun bayan komawarsa kungiyar baya abin kirki wanda hakan yasa kociyan kungiyar zai sayi sabon dan wasan gaba ya rabu dashi. Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal tana fatan sayan Jobic ne domin maye gurbin Pierre-Emerick Aubameyang, wanda ake ganin zai bar kungiyar a karshen wannan kakar sakamakon rashin kokarin kungiyar tun bayan zuwansa. Kamar yadda rahotanni suka bayyana kociyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta, yana shirin sayan Jobic mai shekara 22 a duniya kuma tuni shima dan wasan ya fara tunanin barin Real Madrid saboda kalubalen da yake fuskanta. Jobic ya zura kwallaye 36 cikin wasanni 75 daya bugawa kungiyarsa ta Frankfurt sai dai tun bayan zuwansa Real Madrid ya kasa bayyana kansa duk da wasu suna ganin rashin samun damar buga wasa ne akai-akai yasa baya cin kwallaye.

Kwanakin baya wakilin dan wasan ya bayyana cewa zasu duba yiwuwa barin Real Madrid idan har abubuwa basu canja ba kuma tuni aka bayyana cewa ya fara tattaunawa da wasu kungiyoyin da suka nuna sha'awarsu akan dan wasan dan kasar Serbia. (Saminu, Amina Xu)