Saddam Sani Maidaji: Sinawa sun nuna mini mutunci
2020-04-22 08:32:30 CRI
A cikin shirinmu na wannan mako, wakilinmu Murtala Zhang ya zanta da wani dalibin Najeriya wanda a yanzu haka yake karatun digiri na biyu a bangaren kasuwanci a jami'ar Shenyang dake arewa maso gabashin kasar Sin, wato Malam Saddam Sani Maidaji, kana shugaban kungiyar hadin-gwiwar daliban kasashen waje ta jami'ar. Malam Saddam Sani Maidaji ya ce, cutar numfashi ta COVID-19 na samun sauki sosai a kasar Sin duba da irin managartan matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka, kuma kasashen Afirka suna iya yin koyi daga dabarun kasar.
Har wa yau, Saddam Sani Maidaji ya ce, ya ziyarci birane daban-daban a kasar Sin, inda a ganinsa, Sinawa mutane ne masu mutunci da son baki 'yan kasashen waje, musamman bakaken fata.(Murtala Zhang)