Shawarwari 4 na shugaba Xi Jinping kan yaki da COVID-19 yayin taron G20
2020-04-16 09:41:21 CRI
A ranar Alhamis 26 ga watan Maris na shekarar 2020 ne, aka shirya taron musamman na shugabannin kungiyar G20 kan yadda za a dauki matakan yaki da cutar COVID-19. A wannan karon taron ya gudana ne ta kafar bidiyo saboda annobar da duniya ke fama da ita.
A jawabinsa yayin taron, shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya gabatar da shawarwari 4. Na farko, a daura niyyar hana yaduwar annobar a duk fadin duniya da shirya taron ministocin kiwon lafiya na kasashe mambobin kungiyar G20, sannan a karfafa aikin cin gajiyar bayanai da kuma yin hadin gwiwa wajen nazarin magani da allurar rigakafin annobar. Kana ya za wajibi a hada kai don taimakawa kasashe marasa karfin tattalin arziki wadanda ba su da ingantaccen tsarin kiwon lafiya. Ya kuma yi fatan kungiyar G20 za ta bada shawarar samar da taimakon dakile annobar.
Xi Jinping yana mai cewa, "Bisa tunanin bunkasa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama, bangaren Sin yana son samarwa sauran kasashen duniya managartan matakan rigakafi da kuma dakile cutar, tare da yin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya wajen nazarin magunguna da alluran rigakafin annobar. Bugu da kari, kasarsa za ta taimakawa wasu kasashe da wannan annoba ta barke gwargwadon karfinta.
Na biyu shi ne. Bangaren Sin ya budewa duniya shafin intanet, inda za a iya samun fasahohin rigakafi da dakile cutar COVID-19. Haka kuma, ya kamata kasashen duniya su hada kai domin hanzarta nazarin magunguna da allurar rigakafin cutar da ma binciken cutar. Bugu da kari kuma, ya kamata a tattauna kan yiyuwar kafa tsarin yin mu'amalar harkokin tsaron kiwon lafiyar al'umma na shiyya-shiyya.
Na uku shi ne, bangaren Sin na nuna goyon baya ga kungiyoyin kasa da kasa da su taka rawar gani kamar yadda ya kamata. Bangaren Sin na goyon bayan hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta jagoranci da tsara manufofin rigakafi da kuma dakile cutar bisa ilmin kimiyya, domin kara kokarin hana yaduwar annobar tsakanin kasashen duniya. Ya kamata kungiyar G20 ta karfafa aikin cin gajiyar bayanan rigakafi da kuma dakile cutar, sannan ta fitar da matakan da suka dace wajen dakile cutar baki daya. Na hudu shi ne, kara daidaita manyan manufofin tattalin arziki tsakanin kasa da kasa. Xi Jinping ya nuna cewa, ya kamata kasashen duniya su yi hadin gwiwa wajen daukar matakan nuna adawa da asarar da aka haifar musu domin hana raguwar ci gaban tattalin arzikin duniya.
Taron da kasar Saudiya ta jagoranta, kasancewar shugabar wannan kungiya ta wannan karo, shi ne na farko da kungiyar ta shirya ta kafar bidiyo. Masu fashin baki na fatan shawarwarin da aka gabatar, za su taimaka wajen ganin bayan wannan annoba da ma raya tattalin arzikin duniya baki daya. (Ahmed, Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)