Wasan Tai Chi da wasan Tai Chi tare da mafifici
2020-04-16 14:29:57 CRI
Yang Dezhan, dan wasan Tai Chi na salon "Shadow Tai Chi" na kasar Sin ne, wanda ya taba zama zakara a gasar wasan Kongfu ta kasar Sin, ya kuma taba zama zakara a gasar wasan Tai Chi ta duniya. Yayin da nake zantawa da shi, ya gaya mini cewa, salon Shadow Tai Chi da yake yi, wani tsari ne na horaswar da wasan Tai Chi ne mai sauki. Yayin da ake buga irin wannan salon wasan Tai Chi bisa matakai 10, sannu a hankali za a gano yadda ake yin duk wasan Tai Chi. Ya ce, yayin da ake yin salonsa na wasan Shadow Tai Chi, za a iya yin wasan daga fannoni hudu, wato kiwon lafiya, da gwada fasahohi, da yin amfani da shi a zaman rayuwa, da kuma gano tunanin wasan Tai Chi. Ya ce, wasan Tai Chi yana da dogon tarihi, an kuma fara shi a karshen daular Ming ta kasar Sin. Akwai wani karin magana a zamantakewar al'umma ta lokacin dake cewa, "ba a iya gama koyon wasan Tai Chi sai bayan shekaru 10". Wato duk malamin da ke koyawa wani mutum wasan Tai Chi, ya kamata ya kwashe a kalla shekaru 10 tare da wannan mutum kafin ya gama koyar da shi wasan Tai Chi. Wannan lokaci ne mai tsawo, shi yasa ba a iya yada wasan Tai Chi cikin sauri. Malam Yang ya ce, yana son kafa tsarin wasan Tai Chi ga hanyar kafa salon Shadow Tai Chi da ya buga. Ta yadda ake buga wasan Tai Chi, za a iya gano tunanin Tai Chi na kasar Sin. Yang Dezhan ya bayyana cewa, "Wasan Tai Chi yana da tarihi na shekaru 400 ko fiye kacal, amma tunanin Tai Chi na kasar Sin yana da dogon tarihi na shekaru kimanin dubu 5. Bisa tunanin Tai Chi, an ce kowane batu yana da fuska biyu, kamar yadda muka sani, akwai dare da kuma rana, akwai maza da kuma mata." Yayin da ziyarci yankin Hawaii na kasar Amurka, tare da masu koyon salon wasansa, ya gano hakikanin 'yan kasashen waje su ma suna son irin wannan wasan gargajiya na kasar Sin, haka kuma sun fi son al'adun gargajiya na kasar Sin. A lokacin, ya bayyana cewa, dan Adam na zama a duniya, da muna da asali daban daban, da harsunan daban daban, da kuma al'adun daban daban. Amma dukkanmu muna da buri iri daya, wato kiwon lafiya da jin dadin zaman rayuwa. Ya ce, wasan Tai Chi na iya taimakawa dan Adam wajen kiyaye lafiyar jikinsu, haka kuma tunanin Tai Chi na kasar Sin na iya kwantar da hankalin jama'a, da kyautata hanyar zaman rayuwarsu. Ta yin wasan Tai Chi, yana fatan jama'a za su ji dadin zaman rayuwa, da samun jituwa a duniya baki daya. Yayin da ake tinkarar cutar COVID-19 a dukkan duniya, malam Yang ya bayyana cewa, ya kamata jama'a su yi wasan Tai Chi don kiwon lafiya. Ya ce, "Ya kamata a zabi wani karamin wuri a cikin gida, da yin wasan Tai Chi a gida a wannan lokaci. Ta hakan, za a iya kara karfin numfashi da zuciya da kuma jini, da inganta lafiyar jikin al'umma. Ana iya ganin cewa, wadanda ke yin wasannin motsa jiki musamman wasan Kongfu sun fi samun karfi a jikinsu, da kuma ganin karin haske kan fuskarsa. Kuma ina fatan zan iya yada wannan wasa da tunaninsa, don sa karin mutane su san wannan wasa da tunaninsa, da kara kiwon lafiyarsu ta wasan." Game da yadda za a yada wannan wasan, malam Yang ya fadi shirinsa, wato za a zabi birane 100 na duniya, inda za a nemi masu sha'awar wasan Tai Chi guda miliyan 1, ciki har da mashahuran mutane, ko ma'aikata, ko manoma, da sauran mutane daga bangarori daban daban,da sa dukkansu su yi wasan Tai Chi a sa'i daya, don kafa sabon matsayin bajimtar Guinness a wannan fanni. Gong Nana, wata ma'aikaciyar kamfanin hada-hadar kudi da zuba jari na kasar Sin ce da ta fara nuna sha'awar al'adun gargajiya na kasar Sin a shekarar 2016, a lokacin ta fara koyon wasu dambe iri iri na wasan Kongfu na kasar Sin. Kuma ta fara son yin wasan Tai Chi a watan Mayu na shekarar bara, tana yin wasan a kowace rana. Malam Yang ya koyar sa ita wasan Shadow Tai Chi, a ganinta wasan Tai Chi wasa ne da tsofaffi suke bugawa, amma wannan salon wasan da malam Yang ya kafa ya dace da yanayin matasa, da kara jawo hankalin matasa da su fara yin wasan. Game da canjin da ta samu bayan da ta koyi wasan Tai Chi, ta ce wasan ya canja yanayin jinkinta sosai. Ta ce, "Wasan ya kawo mana babban canji. Da farko dai, numfashi da jini sun kara samun karfi, kana na rage kiba da kilogram fiye da 20, domin ina yin wasan a kowace rana. Kana bayan da na yi wasan, na fara sanin tunanin Tai Chi sannu a hankali, da kwantar da hankalina, da kuma kara fahimtar al'adun gargajiya na kasar Sin."