Ali Albade: Dan Nijar dake aikin sa-kai wajen dakile cutar COVID-19 a kasar Sin
2020-04-15 10:16:15 CRI
A yankin Haidian na Beijing, fadar mulkin kasar Sin, akwai wani dan Jamhuriyar Nijar, mai suna Ali Albade, wanda ya shafe shekaru 11 yana karatu da aiki a nan. Wani abun burgewa shi ne, a lokacin da kasar Sin ke kokarin yaki da cutar numfashi ta COVID-19, wannan bawan Allah wato Ali Albade yana amfani da basirar da Allah ya ba shi a fannin yare, domin tallafawa mazauna unguwarsa yaki da cutar. To, me ya ba Ali Albade sha'awar yin karatu a nan kasar Sin? Ina dalilin da ya sa ya kuduri aniyar gudanar da aikin sa-kai wajen dakile cutar COVID-19 tare da mutanen kasar Sin? Sa'annan a idon mutanen kasar Sin, wane irin mutum ne malam Ali? Wace irin gudummawa yake bayarwa? Ku kade kunnuwanku ku saurari shirin na yau na Sin da Afirka, tare da malam Ali Albade da wakilinmu Murtala Zhang.(Murtala Zhang)