logo

HAUSA

Yadda kamfanoni ke dawowa bakin aiki a kasar Sin

2020-04-09 09:25:58 CRI

Gwamnatocin a sassa daban daban na kasar Sin, sun fito da tarin matakan hanzarta farfado da ayyukan masana'antu wadanda suka gamu da illoli sakamakon barkewar cutar numfashi ta COVID-19. Wasu kamfanoni wadanda suke kokarin gina wasu muhimman manyan ayyukan yau da kullum suna kokarin komawa bakin aiki a lokacin da suke kokarin yakar cutar.

A birnin Shanghai, kungiyoyin nazari da kuma kera jirgin saman fasinja samfurin C-919, da ARJ21, da kuma C-929, sun hanzarta komawa bakin aikinsu domin kokarin samun sabon ci gaba kamar yadda suka shirya, wajen nazari da yin gwaje-gwaje, da kuma kera wadannan jiragen saman fasinja.

Kamfanin kera na'urorin daidaita wutar lantarki na Samsung na kasar Koriya ta Kudu dake yankin masana'antun birnin Suzhou na lardin Jiangsu na kasar Sin yana samar da kaso 20 bisa 100 na masarrafar adana bayanan kwanfuta da ake bukata a fadin duniya, adadin ma'aikatan kamfanin wadanda suka dawo bakin aiki ya kai kaso 95.1 bisa dari na daukacin ma'aikatan kamfanin, Yayin da kamfanonin ke kamowa bakin aiki, a hannu guda kuma ana daukar matakan kula da lafiyar ma'aikata, kafin su koma wuraren ayyukansu.

Alkaluma sun nuna cewa,kaso 90 bisa dari na manyan masana'antun kasar dake a matsayi na larduna, ban da Hubei inda cutar ta fi kamari, sun koma bakin aiki bayan fama da cutar numfashi ta COVID-19, wanda hakan sakamako ne na matakan farfado da ayyuka da yankunan kasar daban daban suke aiwatarwa.

Kusan kaso 100 bisa 100 na masana'antun dake lardin Zhejiang, da Jiangsu, da Shanghai, da Shandong, da Guangxi, da Chongqing sun kammala komawa bakin aiki.

Alkaluman amfani da lantarki a yankunan, sun nuna yadda muhimman sassan sarrafa hajojin masana'antu ke farfadowa. Kaza lika kamfanonin sarrafa karafa sun koma aiki gadan gadan kamar yadda suke yi a shekarar bara, yayin da kamfanonin harhada magunguna, da na hada sinadarai, da kamfanonin laturoni, suka fara amfani da lantarkin da ya kai kaso 90 bisa dari, na yawan lantarkin da suke amfani da shi kafin aukuwar wannan annoba. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)