logo

HAUSA

Hira tare da malama Fatima Liu, wadda ke koyar da harshen Hausa a jami'ar koyon harsunan waje ta Tianjin

2020-04-07 13:22:17 CRI

 

Malama Fatima Liu (Hudu a hagu) da malam NuraddeenIbrahim Adam (Tsakiya) da dalibansu

 

Wasu tsoffin masu sauraronmu, sun dade suna mu'amala da malama Fatima Liu, tsohuwar abokiyar aikinmu a sashen Hausa na CRI. Bayan da aka bude sashen koyar da harshen Hausa a jami'ar koyon harsunan waje ta Tianjin, sai aka neman malaman da za su koyar da harshen, wannan ya sa aka gayyaci malama Fatima Liu don ta koyar a jami'ar. Kwanan baya, na yi hira da ita, inda muka tattauna game da zaman rayuwarta da yadda take aikin koyarwa yanzu, a wannan lokaci na musamman na tinkarar cutar numfashi ta COVID-19. To, a cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku bayani ne game da wannan batu.