logo

HAUSA

Kantin kasa da kasa ya farfado<?xml:namespace prefix = o ns = "urn:schemas-microsoft-com:office:office" />

2020-04-03 15:40:56 CRI

Kantin kasa da kasa ya farfado<?xml:namespace prefix = o ns = "urn:schemas-microsoft-com:office:office" />

Muhammadu Naziru

Birnin Yiwu da ke lardin Zhejiang na kasar Sin birni ne da ake masa lakabin "World SuperMarket", wato babban kantin kasa da kasa, a sabili da kasancewar babbar kasuwar sayar da kayayyaki kala kala a wurin, kuma baki 'yan kasuwa da suka zo daga kasa da kasa na zuwa wajen yin ciniki, 'yan kasuwar kasashen Afirka ma ba a bar su a baya ba, kuma malam Muhammadu Naziru da Shazali Yawu na daga cikinsu.

Kantin kasa da kasa ya farfado<?xml:namespace prefix = o ns = "urn:schemas-microsoft-com:office:office" />

Shazali Yawu

Bayan da aka samu sassaucin yanayin cutar numfashi ta Covid-19 a nan kasar Sin, kamfanoni da masana'antun da suka farfado da harkokinsu suna ta karuwa, kuma a ranar 18 ga watan Faburairun da ya wuce, an sake bude kasuwar. Shin yaya harkoki ke gudana a kasuwar? A biyo mu cikin shirin, don jin ta bakin malam Muhammadu Naziru da malam Shazali Yawu.(Lubabatu)