Hadin gwiwar Sin da Afirka wajen yaki da COVID-19
2020-04-02 08:47:42 CRI
A kwanakin baya ne gwamnatin kasar Sin ta gudanar da hadin gwiwa da kasashen Afirka, Turai da Asiya wajen yin kandagarki da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19.
Yayin wani taron manema labaran da aka kira , mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Geng Shuang ya ce, kasar Sin da kasashen Afirka sun shirya wani taron kwararru ta kafar bidiyo kan yadda za a yi aikin kandagarki da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19.
Jami'ai da kwararru kimanin 300 na kasashen Afirka da suka halarci wannan taro, sun nuna yabo matuka kan babban sakamakon da kasar Sin ta samu wajen yaki da cutar, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye tsaron lafiyar al'ummar duniya. Sun kara da cewa, taron ya zo a lokacin da ya dace, kuma sun amfana kwarai da gaske. kasar Sin tana son ba da karin gudummawa wajen tunkarar kalubalen lafiyar al'umma da duniya ke fuskanta, da kare muradun bil-Adama ta hanyar kungiyoyi kamar G20. Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta ce aikin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 da ake gudanarwa a Afrika ya samu tagomashi bayan samun tallafin kayayyakin kiwon lafiya daga gidauniyar Jack Ma da ta Alibaba.
Tallafin kayayyakin kiwon lafiyar wanda gidauniyar babban attajirin dan kasar Sin Jack Ma ta bayar domin rabawa ga kasashen Afrika 54 ya riga ya shoga hannun kasashen na Afirka, har ma sun fara amfani da su.
Tallafin ya hada da kayayyakin rufe baki da hanci kimanin 100,000, da kayayyakin gwaje gwaje 20,000, da kuma rigunan ba da kariya 1,000 ga ko wace kasa daga cikin kasashen Afrika 54.
A wani bangare na taimakon da kasar Sin ke ba nahiyar Afrika wajen dakile yaduwar cutar, kwararru da jami'an lafiya da na kwastam na kasar, sun gabatar da bayanai game da yadda suka fuskanci cutar COVID-19 a wani taro da aka yi ta kafar bidiyo da jami'ai da kwararrun kan kiwon lafiya daga cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Afrika CDC da na wasu kasashen nahiyar 24, lamarin da ya nuna kudurin kasar Sin na bayar da bayanai da taimakon nahiyar a yaki da annobar. (Ahmed, Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)