logo

HAUSA

Masu sha'awar wasanni na ci gaba da motsa jiki a lokacin da ake tinkarar cutar COVID-19

2020-03-27 16:01:02 CRI

Yanzu haka annobar cutar numfashi ta COVID-19 tana yaduwa a sassa daban daban na duniya. Likitocin kasar Sin da dama da suka shiga ayyukan yaki da cutar a kasar sun tafi ketare domin taimakawa takwarorinsu na kasashen waje, ko kuma sun yi karin bayani kan fasahohin yaki da cutar cikin hoton bidiyo kan Internet. A halin yanzu, kasar Sin ta samu nasarori wajen yaki da cutar COVID-19, ba a samu rahoton sabbin wadanda suka kamu da COVID-19 a Wuhan ba cikin wasu kwanaki a jere, kana harkokin rayuwar jama'a a dukkan wuraren kasar Sin na kara dawowa kamar yadda suke a baya. A kokarin da ake na hana yaduwar cutar, wasu Sinawa masu sha'awar wasannin motsa jiki sun dakatar da motsa jiki a waje a wannan lokaci. Amma suna ci gaba da motsa jiki ta wasu hanyoyi marasa hadarin kamuwa da cutar.

Masu sha'awar wasanni na ci gaba da motsa jiki a lokacin da ake tinkarar cutar COVID-19

Mai Sha'awar Wasan Kwallon Kafa Wang Zixin

Wang Zixin, dan jarida a wani gidan rediyon kasar Sin ne, kuma mai sha'awar wasan kwallon kafa, da kwallon kwando, da wasan badminton, har ma da wasan guje-guje. Amma ya fi sha'awar wasan kwallon kafa, ya kuma shafe shekaru da dama yana wannan wasa. Kafin barkewar cutar COVID-19, ya kan buga wasan kwallon kafa sau biyu ko uku a kowane mako. Yana kuma shafe tsawon sa'o'i biyu zuwa uku. A ganinsa, a matsayinsa na dan jarida, ya kan zauna a cikin ofis kuma babu lokacin motsa jiki, zai kula da lafiyar jikinsa ta hanyar wasan kwallon kafa, kana yana jin dadi yayin da yake wasan. Ya ce, wasan kwallon kafa wasa ne da ake bukatar mutane da dama su yi wasa tare, don haka ya iya samun abokan da za su yi wasan tare.

A yayin da cutar COVID-19 ta fara yaduwa a kasar Sin, shi da abokan wasan kwallon kafansa sun dakatar da wasan. Amma duk da haka, ya zabi wasu hanyoyi domin ci gaba da motsa jiki. Wang Zixin yace, "Yayin da cutar COVID-19 ta barke, mun dakatar da buga wasan kwallon kafa domin wasan kwallon kafa wasa ne da ya kunshi mutane da dama. Don haka, a halin yanzu mun koma yin guje-guje a maimakon wasan kwallon kafa. A ganina, guje-guje suna da nasaba da dukkan wasannin motsa jiki, kana mutum daya ma yana iya yi, ba bukatar da yin mu'amala da sauran mutane." Wang Zixin ya kara da cewa, koda yake an samu manyan nasarori wajen yaki da cutar COVID-19, da samun farfadowar harkokin rayuwa na yau da kullum, amma ba a kawo karshen yaki da cutar ba. Ya kamata kowa da kowa ya martaba matakan magance yaduwar cutar, don haka bai fara buga wasan kwallon kafa tare da abokansa ba, maimaikon haka, ya ci gaba da yin guje-guje don kiyaye koshin lafiya. Wang Zixin yana ganin cewa, motsa jiki ita ce muhimmiyar hanyar tinkarar cututtuka, da kwantar da hankulan jama'a, da kara karfin jiki, da kuma kiyaye lafiyar dan Adam. Yana fatan za a kawo karshen yaki da cutar COVID-19 cikin hanzari, da dawo da harkokin wasannin motsa jiki iri iri kamar yadda aka saba kafin barkewar cutar. Ya ce,   "Bayan da aka cimma nasarar yaki da cutar, ina fatan za a bude wuraren wasannin motsa jiki, ko kuma a kayyade yawan mutanen da za su shiga wuraren wasannin motsa jiki, ta yadda za mu ci gaba da motsa jiki a waje. Amma game da wasu dakunan wasannin motsa jiki, ya kamata a jinkirta bude su, a ganinta hakan zai iya bada kariya ga masu sha'awar wasannin motsa jiki."