Shin ya kamata mu yi ma Yaran Maza tarbiyan ayyukan gida, ko kuwa sai 'ya Mace kawai za mu yi ma wannan tarbiyar?
2020-03-26 12:49:44 CRI
A cikin wannan sabon shiri na Ra'ayi na, baki wadanda suka halarci tattaunawa sun yi musayar ra'ayoyinsu kan batun "shin ya kamata mu yi ma Yaran Maza tarbiyan ayyukan gida, ko kuwa sai 'ya Mace kawai za mu yi ma wannan tarbiyar?"
Kuma a yau Bakin da za su taya mu muhawara a cikin shirin na Ra'ayi na su ne Hajia Hauwa Ibrahim Bello da Malam Ali Uba Taura wadanda kowannensu zai yi iyakacin kokarin kare matsayar da ya zaba.
Hajia Hauwa Ibarhim Bello dai tana kan matsayar cewa wannan hakki ne da ya ta'allaka a kan 'ya Mace, wato ayyukan gida a bar Yara Maza su yi wassu hidimomin da ya kamance su, amma ban da cikin gida Shi kuma Malam Ali Uba Taura ya dage a kan cewa ba haka ba ne, ganin yadda rayuwa ta kasance a yau din nan yana da muhimmanci a yi ma Yara maza tarbiyar na koyon ayyukan gida tun da kamar addininmu ma ya nuna mana hakan. (Ibrahim Yaya, Fatimah Jibril)