Yi iyakacin kokari don kiyaye tsaron lafiyar dan Adam
2020-03-24 14:38:39 CRI
Lardin Henan, yanki ne dake dab da lardin Hubei, wanda ya fi fama da cutar numfashi ta COVID-19 a nan kasar Sin. Don haka, tun daga lokacin farkon da aka bullar cutar a kasar, lardin Henan ya dauki jerin matakai masu dacewa cikin lokaci don tinkarar annobar, ciki har da dakatar da motocin kwashe ma'aikata, kara asibitoci masu karbar wadanda suka kamu da cutar har zuwa 130, auna zafin jikin mutane a wasu muhimman hanyoyin mota, kashe kwayoyin cuta a tashoshin jiragen kasa karkashin kasa da unguwanni, da kuma sanar da ilmi game da cutar ta hanyoyi daban daban da dai sauransu. Kamar yadda masu kallo yanar gizo na kasar Sin suka ce, lardin Henan ya dauki matakai masu amfani cikin sauri, har sun kasance abin koyi ne a fannin kandagarki da shawo kan annobar. Ko shakka babu dukkan matakan ake gudanar da su ne gwargwadon kokarin da ake yi daga bangarori daban daban, ciki har da 'yan uwanmu mata. A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku bayani ne game da 'yan uwa mata biyu dake taka rawarsu a yayin da ake tinkarar annobar.
Wang Shuo, 'yar shekaru 30 a duniya, 'yar sanda ce dake kula da harkokin ofishi na rukuni na tara na reshin kungiyar 'yan sanda dake aiki a jiragen kasa. Abokan aikinta suna kiranta "Uwar gida mai kula da aikin yaki da annoba ta kungiyar 'yan sandan". Bayan bullar cutar numfashin, sai ta gabatar da bukatun shiga kungiyar 'yan jam'iyyar kwaminis masu yaki da annoba.
"'Kamata ya yi 'yan jam'iyyar kwaminis su kasance a kan gaba a yayin da ake tinkarar annoba', wannan shi ne nufinmu na kafa kungiyar 'yan jam'iyya masu yaki da annoba. A matsayi na yar jam'iyya, ko da yake ban fara zuwa fagen yaki ba, amma abun da ya kamata na yi a wannan muhimmin lokaci shi ne, na ba da cikakken tabbaci a fannin guzuri ga abokan aiki na 'yan sanda. Don haka, na shiga wannan kungiya, na kuma hada da 'yan sanda dake aiki a jiragen kasa don tsaron rayuwar jama'a."
Malama Wang Shuo dake aiki
A ko wace rana da safe, kafin abokan aikinta suka zo aiki, sai ta fara binciken kayayyakin kiyaye tsaron lafiya da 'yan sandan dake aiki a jiragen kasa ke bukata, don tabbatar da tsaron lafiyarsu. A cewar Wang Shuo,
"Ma'aunin bukatun ayyukanmu na yau da kullum ya karu sosai a kan na da. Muhimman ayyuka na shi ne, ba da tabbacin guzuri ga 'yan sanda dake aiki a jiragen kasa, ciki har da ba su abun rufe baki da hanci, safar hannu, da wasu kayayyakin kare lafiya, kana da gudanar da aikin kashe kwayoyin cuta da auna zafin jikin 'yan sandan, don tabbatar da tsaron lafiyarsu. Idan har na gudanar da wadannan ayyuka yadda ya kamata, za mu kawar da damuwar da 'yan sanda ke fuskanta, ta yadda za su iya gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. "
Sakamakon halin ayyukansu, Wang Shuo ta dade ba ta tafi gidan iyayenta don nuna gaisuwa ba. Ta ce,
"Babbar wahalar da nake fuskanta a yayin da nake aiki ita ce, damuwa daga iyalina, ina aiki ne a tashar jiragen kasa ta gabas ta birnin Zhengzhou, akwai mutanen da yawa a nan, don haka ina cudanya da mutane da dama a ko wace rana. Don rage hadarin da zai iya haifarwa iyali na, tun lokacin da cutar ta barke zuwa yanzu, ban taba komawa gidan iyaye na ba, sai dai na buga musu waya. Amma, na yi imanin cewa, bisa kokarin da daukacin al'umma suka yi, ba shakka za a ci nasarar yaki da cutar."
Game da ayyukan da Wang Shuo ke yi a yayin kandagarki da shawo kan cutar numfashin, mijinta Zhu Hengwei, ya ce, da farko ya damu sosai,
"Saboda muhimman ayyukanta su ne ba da tabbaci na guzuri ga 'yan sanda dake aiki a jiragen kasa, wadanda suka fi hadarin kamu wa da cutar. Amma, daga baya, a yayin da nake kallon talibijin, na ga wasu labarai game da likitoci da nas nas, wadanda ba sa tare da iyalansu, kuma suna fuskantar hadari mai tsanani don ci gaba da ayyukansu na ceton jama'a, ganin haka, na fahimci cewa, ya kamata na goyi bayan aikin da mata ta take yi."
Don haka, Zhu Hengwei ya tsaida kudurin kai matarsa da dawo da ita daga aiki a ko wace rana, ya ce,
"Ni ma na ba da nawa tallafin, da tabbacin guzuri ga mata ta, hakan mata ta ta iya ba da hidima yadda ya kamata ga abokan aikinta 'yan sanda."
Birnin Xinyang, yana kudancin lardin Henan, wanda kuma ya fi dab da lardin Hubei da cutar COVID-19 ta fi kamari, don haka mutane masu yawa na birnin Xinyang suna son aiki a Wuhan, kuma mutanen lardunan biyu suna kai da dawowa ta wannan birnin. Bayan bullar cutar, birnin Xinyang ya kasance wurin da aka fi fama da cutar a lardin Henan, ko shakka babu nauyin dake kan wuyan likitoci da nas nas dake aiki a asibitocin wurin, ya karu matuka. Xi Lei, tana daya daga cikinsu.
Xi Lei (Hagu) da abokiyar aikinta
Xi Lei, yar shekaru 43 a duniya, wadda ke aiki a aisibitin Renmin na birnin Xinyang, muhimmin aikinta shi ne, tattara da tsara bayyanai game da yadda masu kamu da ciwo ke samun jinya a asibitinsu. Ta gaya mana cewa, a ranar 24 ga watan Faburairun na bana, wato jajibirin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, dukkan ma'aikatan asibitin sun samu wata sanarwar gaggawa ta soke lokacin hutu na bikin bazara, da kuma soma aiki ba tare da bata lokaci ba saboda yaduwar cutar COVID-19.
"Bisa tsanantar yanayin annobar, ba mu da isassun kayayyakin ba da kariya daga cututtuka, har ma ba mu da abubuwan rufe baki da hanci. Domin tabbatar da lafiyar likitoci da nas nas, musamman wadanda ke ba da jinya ga masu kamu da cutar, da rage nauyin dake kan asibitinmu, sai na yi ta kokari domin neman hanyar sayen kayayyakin ba da kariya."
Xi Lei ta ce, a farkon bullar cutar, ta yi dan damuwa kan yiwuwar kamu da cutar, saboda ba ta son yada cutar ga iyalanta.
"Sashen kula da masu kamu da ciwon COVID-19 dake cikin mawuyacin hali yana kusa da ofishinmu, inda cike da wadanda suka kamu da ciwon, a lokacin farko kuma, ba a dauki matakai masu dacewa sosai ba a yayin da ake yaki da cutar, don haka, na yi dan damuwa. "
Kamar yadda mijin Wang Shuo yake, mijin Xi Lei ma yana kai matarsa da dawo da ita daga aiki a ko wace rana, ban da wannan kuma bayan Xi Lei ta koma gida, sai ya riga ya dafa abinci masu dadi. A cewar Xi Lei,
"Lallai, nauyin dake bisa wuya na a matsayin wata likita, da kulwa da rakiya daga wajen iyalina, suna goyon baya na wajen tsaya kan aikina yadda ya kamata."
Sakamakon kokarin da take yi, kwamitin tsakiyar jam'iyyar demokuradiyya ta CPWDP, ta rubuta mata wata wasikar godiya don nuna mata yabo wajen yaki da cutar COVOD-19.
"A gani na, abubuwan da na yi ba su tantanci irin yabo ba, na gudanar da aiki ne da kamata ya yin a yi." (Bilkisu)