logo

HAUSA

Hira da Yahaya Baba ma'aikace a kamfanin StarTimes

2020-03-19 11:25:37 cri

A yayin da hukumar lafiya da duniya WHO a takaice, ta ayyana cutar numfashi ta COVID-19 a matsayin annobar da ta shafi duniya baki daya. A hannu guda kuma kasar Sin ta fita daga kololuwar yaduwar cutar.

Masana harkar kiwon lafiya sun bayyana cewa, idan har kasashe da dama na duniya suka dauki managartan matakai kamar yadda kasar Sin ta yi, hakika za a shawo kan cutar nan da 'yan watanni.

Bayanai na nuna cewa, a nan kasar Sin, ana ci gaba da samun raguwar sabbin mutane dake kamuwa da cutar, kuma baki dayan yanayin annobar na raguwa matuka. Kan haka ne abokin aikinmu Ibrahim Yaya, ya zanta da Malam Yahaya Baba dake aiki a kamfanin StarTimes dake birnin Beijing, kan irin matakan da kamfanin nasu yake dauka wajen dakile wannan cuta. Amma ya fara da tambayarsa kan halin da ake ciki a wajen aikin nasu.

 

Hira da Yahaya Baba ma'aikace a kamfanin StarTimes