logo

HAUSA

Zhang Weili, zakarar gasar damben UFC na fatan karfafawa 'yan mata gwiwa

2020-03-18 08:38:45 CRI

A kwanan baya wato ranar 8 ga watan Maris, wata Basiniya ta zama zakarar gasar damben UFC na ajin mafi kankantar nauyi, bayan ta doke abokiyar karawarta Joanna Jedrzejczyk ta Poland, yayin gasar dambe ta UFC da aka yi a birnin Las Vegas a gasar UFC ta 248. Sunan macen shi ne Zhang Weili, wadda ta kasance Basiniya ta farko da ta lashe kambin damben UFC na duniya.

Yayin da ta zantawa da manema labrai, Zhang ta ce, ta yi kokari sosai wajen zaman zakarar. Kuma tana fatan, za ta iya ba karin 'yan mata kwarin gwiwa domin su zaman jajirtattu masu cimma burinsu. (Kande Gao)