Likitancin gargajiya na kasar Sin zai taimaka ga inganta tsarin garkuwar jikin dan Adam a Najeriya
2020-03-18 08:38:52 CRI
A halin yanzu cutar numfashi ta COVID-19 ko kuma coronavirus na ci gaba da bazuwa a kasashen duniya da dama, duk da cewa cutar na samun sauki sosai a nan kasar Sin, duba da irin managartan matakan da gwamnatin kasar ta dauka ba tare da wani jinkiri ba. Kasashen da cutar ta fi kamari sun hada da, Italiya, da Iran, da Koriya ta Kudu, da wasu kasashen Turai, ciki har da Sifaniya, da Burtaniya, da Faransa da sauransu, kasar Amurka ita ma tana fuskantar babbar barazana. Har ma akwai wasu manyan kusoshin gwamnatocin kasashe daban-daban wadanda ke kamuwa da cutar ta COVID-19.
A bangaren Afirka ma, zuwa karshen makon da ya gabata, akwai kasashe sama da 20 wadanda aka samu bullar cutar, ciki har da Aljeriya, da Burkina Faso, da Kamaru, da Kwadibwa, da Jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo, da Masar, da Morocco, da Najeriya, da Senegal, da Afirka ta Kudu, da Togo, da Tunisiya, da Ghana, da Gabon, da Kenya, da Habasha, da Sudan da kuma Guinea. Duk da cewa kawo yanzu mutum dari biyu da wani abu ne suka kamu da cutar a Afirka baki daya, kana akasarinsu sun fara kamuwa da cutar ne a wajen Afirka, wato ba a Afirka suka kamu da cutar ba, amma ana shakkun cewa ko kasashen Afirka na da cikakken karfin tinkarar cutar idan ta ci gaba da yaduwa.
Idan mun dubi matakai iri-iri da gwamnatin kasar Sin ta dauka wajen tinkarar cutar, za mu gano cewa, maganin gargajiya na kasar Sin na taka muhimmiyar rawa. To, menene ainihin amfanin maganin gargajiya na kasar Sin? Ko kasashen Afirka, musamman Najeriya, za su yi amfani da shi wajen dakile yaduwar cutar COVID-19, da kuma sauran wasu cututtuka masu yaduwa? Wakilinmu Murtala Zhang ya zanta da wasu likitoci daga asibitin Eastern and Western Hospital, wato asibitin da ya hada likitancin Turawa da na Sinawa a Abuja, fadar mulkin Najeriya. Ku saurari shirin Sin da Afirka na wannan mako don jin karin bayani!(Murtala Zhang)