logo

HAUSA

Matakan kasar Sin ta tabbatar da zaman lafiya a Xinjiang

2020-03-12 10:04:11 CRI

A kwanakin baya ne, majalisar wakilan Amurka ta zartas da dokar hakkin Bil Adama na kabilar Uygur ta jihar Xinjiang, dokar da ta illata yanayin hakkin Bil Adama a jihar Xinjiang, har ta shafa bakin fenti kan ayykan da Sin take yi na kawar da tsattsauran ra'ayi da ta'addanci, da kuma takalar manufar da gwamnatin Sin ke dauka wajen gudanar da harkokin jihar, matakin da ya keta dokar kasa da kasa da ka'idar dangantakar kasa da kasa, kuma shisshigi ne a harkokin cikin gidan kasar Sin, wanda Sin ba ta ji dadinsa ba, kuma ba za ta yarda da shi ba.

Matakan kasar Sin ta tabbatar da zaman lafiya a Xinjiang

Sannin kowa ne cewa, Jihar Xinjiang ta kasar Sin na fama da masu tsattsauran ra'ayi da ayyukan ta'addanci. Saboda ganin irin hali mai tsanani da take ciki, gwamnatin jihar ta dauki matakan da suka dace don dakile su, a sa'i daya kuma, tana mai da hankali kan kawar da asalin wadannan mummunan ayyuka, ciki hadda sa kaimi ga aikin kawar da tsattsauran ra'ayi, matakin da ya ba da tabbacin cewa, ba a samu ayyukan ta'addanci a jihar ba har tsawon shekaru 3 a jere, hakan ya sa mutanen jihar miliyan 25 ke farin ciki sosai da maraba da wadannan manufofi, matakin da ya taka rawa ga aikin yaki da ta'addanci a duniya.

Matakan kasar Sin ta tabbatar da zaman lafiya a Xinjiang

Ban da wannan kuma, kasashen duniya na yabawa wadannan manufofi sosai. Saboda haka, matakin da Amurka ta dauka ya sabawa hakikanin halin da ake ciki da ra'ayin al'ummar duniya, Harkokin jihar Xinjiang harkokin cikin gidan kasar Sin ne, ba wanda zai iya tsoma baki a ciki. Wannan ya sa kasar Sin, ta yi kira ga Amurka da ta gyara kuskurenta, tare da dakatar da zartas da wannan doka da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, kana kasar Sin, za ta mayar da martani ga duk matakin da Amurka za ta dauka. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)