logo

HAUSA

Ko aikin gwamnati da kuma aikin kanka da kanka wane ne ya fi muhimmanci?

2020-03-05 09:22:11 CRI

A cikin wannan sabon shiri na Duniyarmu A Yau, baki wadanda suka halarci tattaunawa sun yi musayar ra'ayoyinsu kan batun "Aikin gwamnati da kuma aikin kanka da kan ka wane ne yafi muhimmanci?

Ko aikin gwamnati da kuma aikin kanka da kanka wane ne ya fi muhimmanci?

Inda Bakin namu a yau Malama Na'imatulla Umar Makada da Malam Ali Uba Taura za su yi muhawara sosai na ganin kowa ya tabbatar da ra'ayin shi ne ya fi dacewa da amsar maudu'in.

A yau Malam Nai'imatulla Umar Mada ta dage a kan ra'ayin ta na cewa aikin kan ka ya fi komai daraja da kwanciyar hankali. Musamman ganin cewa kai ne ke da ikon kan ka a wannan waje babu wani da zai saka yi dole ko ya hana ka, za ka fita aiki lokacin da kake so ka dawo lokacin da kake so in ka ga dama ma ka yi kwanciyar ka kana aiki a gida.

Ko aikin gwamnati da kuma aikin kanka da kanka wane ne ya fi muhimmanci?

Amma shi kuwa Malam Ali Uba Taura yana tare da wannan kirari da Bahushe kan yi ya ce Gwamnati Ikon Allah don haka yana tare da wannan batu yana kuma kan ra'ayin aikin gwamnati na da magogara da ba ka kariya.

Matsayar bakin namu ke nan da dai sauran bayanai da suka yi don kare ra'ayin su. (Saminu, Fatimah, Ali, Sanusi)