Shin Ilimin karatun Jami'a ko amfani da baiwar wane ne yafi muhimmanci?
2020-02-27 13:03:27 CRI
A cikin wannan sabon shiri na Ra'ayi Na A Yau, Malam Muhammed Baba Yahaya da Malam Ali Uba Taura ne bakin na mu wadanda zasu bayyana ra'ayin su tare da yin muhawara sosai na ganin kowa ya tabbatar da dalilin shi ne yake ganin ya dace da amsar maudu'in. "Shin Ilimin karatun Jami'a ko amfani da baiwar wane ne yafi muhimmanci, don samun na rufin asgiri na yau da kullum?
Inda Malam Mohammed Baba Yahaya a yau yake da ra'ayin baiwa da basira yafi maimakon a ce an yi dogara da ilimin digiri na jami'a za'a nemi aikin yi.
Amma shi kuma Malam Ali Uba Taura ya ce a'a a dai yi karatun a samu ilimin digirin wanda shi ne kamar tushen ko wane aiki. An dai buga muhawara inda kowanne daga cikin su ya yi iyakacin kokarin kare matsayar sa a wannan shirin. (Saminu, Fatimah, Sanusi)