Sabuwar hanyar zamani da ake bi wajen ba da ilmi a cikin halin musamman da ake ciki na yaki da cutar numfashi a nan kasar Sin
2020-02-21 18:10:52 CRI
Ko da yake yanayin annobar cutar numfashi ta COVID 19 wadda ke iya yaduwa a tsakanin mutum da mutum, na samun kyautatuwa a nan kasar Sin, amma har yanzu ba a kawo karshen cutar ba a kasar, don haka dukkan makarantun dake fadin kasar Sin sun tsaida kudurin jinkirta lokacin fara zangon karatu. Ba da ilmi, babban aiki ne dake jawo hankulan dubun-dubatan iyalai a nan kasar Sin. Domin kawar da tasirin da annobar ka iya yiwa dalibai kan harkokinsu na karatunsu, an soma ba da darusa ga daliban ta hanyar yanar gizo.
Sakamakon saurin bunkasuwar sha'anin yanar gizo a nan kasar Sin, a 'yan shekarun nan, an kuma samu babban ci gaba wajen ba da ilmi ta kafar yanar gizo, musamman ma a fannin habaka darusa, ya zuwa yanzu, ana iya ba da ilmi mai inganci ta yanar gizo a wurare daban daban masu yawa a kasar. Bisa wannan yanayin da ake ciki na yaki da cutar numfashi, hukumomin ba da ilmi na kasar Sin sun dauki matakin bullo da kwasa-kwasai ta yanar gizo a yawancin yankunan kasar, wannan wani sabon fanni ne da aka gwada a fannin ba da ilmi. To, game da wannan sabuwar hanya ta zamani, mene ne ra'ayoyin ma'amai da dalibai? Kuma ko hanyoyin sun dace ko akwai gyara? Kwanan baya, na buga waya tarho ga wata malama da dalibanta don jin ta bakin su wannan batu.
Zhang, malama ce dake koyarwa a wata makarantar sakandare dake birnin Beijing, ta gaya mana cewa, makarantarsu da malamai sun yi shirya tsaf don ganin sun koyar da daliban yadda ya kamata. Ta gayawa wakiliyarmu cewa, "Makarantarmu ta kafa rukunoni daban daban a yanar gizo don kula da harkokin malamai da na dalibai, kana da kimanta lafiyar tunanin dan Adam cikin lokaci, da koyar da dalibai matakan kiwon lafiya, kana an tsara kwasa-kwasai na wucin gadi, da tsara wasannin ko rawa don motsa jiki da kara lafiya, makarantarmu ta raba wadannan shirye-shiryen tsakanin malamai da na dalibai."
Malama Zhang ta ce, malaman makarantarsu sun soma tsara darusa na musamman ne mako daya kafin a soma koyarwa, an yi haka ne don tabbatar da cewa, ba a dakatar da karatu ba duk da cewa an dakatar da darusa a makarantar.
"Muna amsa tambayoyin dalibai ta hanyar yanar gizo, don taimaka musu warware matsalolin da suke fuskanta a fannin karatu, mun kuma bullo da wasu kwasa-kwasai na musamman bisa hakikanin halin da malamai da dalibai suke ciki, wadanda suka shafi inganta abubuwan da aka koya, kara karatu ta hanyar tattaunawa da nazari, karanta shahararrun litattafan adabi na gargajiya, kara motsa jiki, shiga ayyukan gida na yau da kullum da dai sauransu. "
Malamai da dalibai suna mu'amala ta dandalin sada zumunci na Wechat
Malama Zhang ta kara bayyana cewa, a yayin da ake gudanar da wannan aiki, yanar gizo ta kara saukaka wa malamai yadda suke koyar da dalibansu cikin lokaci, ta hanyar tattauna matsaloli, da musayar ra'ayoyi game da harkokin karatu, irin wannan hanya ta samu karbuwa sosai a wajen dalibai, a ganinsu, wannan sabuwar hanya tana da ban sha'awa, kuma suna son shiga ayyukan da aka tsara musu, hakan ya sa dangantakar dake tsakanin malamai da dalibai ta kara kyautatuwa.
Xu, wata daliba ce dake karatu a wannan makarantar, ta bayyana cewa,
"Makon da ya wuce ne muka soma koyon darusa ta hanyar yanar gizo, Ina ganin hanyar da na saukin koyo, ba kawai tana da amfani wajen kandagarki da shawo kan cutar numfashi ba, har ma ta taimake mu wajen kallon darasi ta bidiyo da aikin da malamanmu suka tsara a duk lokacin da muke so ta intanet, ban da wannan kuma, bayan mun gabatar da aikin gida, malamai suna iya ba mu amsa cikin lokaci."
A nata bangaren, Chen wata daliba dake karatu a makarantar ta gaya mana cewa,
"Irin wannan hanyar ba da darussa ta yanar gizo tana taimaka min wajen kara kwarewa ta ta fahimtar abubuwa da kanmu, tana kuma taimakon mu shafe lokuta mai yawa muna karatu. Muna iya tambayar malamai abubuwan da suke shige mana duhu a duk lokacin da muke bukata, kana muna iya samun abubuwa na fannoni ilimi da dama a yanar gizo, gaskiya hanyar ta kawo mana sauki sosai." Jiang, shi ma dalibi na makarantar, yana ganin cewa, "Ba da darussa ta hanyar yanar gizo ba kawai ya taimaka mana wajen kara inganta abubuwa masu muhimmanci da muka samu ba, har mun tsara lokutan na karatu da na hutu, a baya muna zama dama yin karatu a lokacin hutu na yanayin sanyi, yanzu muna ta kokarin sabawa da darasin, hakan ya sa sannu a hankali mu ka shirya don fara zangon karatu a hukunce. Baya ga haka, kwasa-kwasai daban daban da aka tsara, da isassun lokacin dukkansu sun sa ba ma gajiya a yayin da muke karatu ta hanyar yanar gizo."
Malami ya gyara zane-zanen da dalibai suka yi a yanar gizo
A wasu gidajen, mai yiwuwa akwai bukatar iyaye su fita waje don gudanar da aiki, hakan ya sa watakila yara su manta da lokaci, ko su yi wasa kawai. To, yaya za a warware irin wannan matsala? Malama Zhang ta gaya mana cewa, game da irin wannan halin da ake ciki, malamai sun raba dalibai zuwa rukunoni daban daban masu yawa, sun kuma mu'amala da juna game da harkokin karatu, an kuma ba su wasu batutuwa don su yi nazari da tattaunawa a kansu.
A karshen zantawar, malama Zhang ta ce,
"Yaran suna jin dadin karatu sakamakon yadda suke nuna da'a a lokacin da suke koyo a wannan lokacin na musamman, suna darajanta zumunci, kuma wannan ya shiga cikin zukatansu sakamakon jagoranci da malamai suke ba su, da kulawa da iyayensu suke ba su. Ta hanyar dandalin sada zumunta na Wechat, su kan gaya min cewa, 'Malama, ina tunaninki, ina son na komo makaranta!' Na yi imanin cewa, bayan wannan yanayin annobar, yaran za su kara imani da kan su. Kuma dukkan Sinawa za su kara tsayawa kan niyyarsu kuma cike da kyakkyawar fata kan makomarsu. "