Yara da ake cin zalinsu, ya kamata su kai kara ko su rama?
2020-02-20 17:24:29 CRI
A cikin wannan sabon shiri na Duniyarmu A Yau, baki wadanda suka halarci tattaunawa sun yi musayar ra'ayoyinsu kan batun ko "Yara da ake cin zalinsu, ya kamata su kai kara ko su rama?" inda Hajiya Hauwa Ibrahim Bello da malam Yahaya Babs suka yi musayar ra'ayoyinsu sosai.
A ganin hajiya Hauwa, idan aka cin zalin yaronta, ya kamata yaronta ya rama. Ta kara da cewa, duk inda kake kana kokarin sa kunne kaji naka ya yi abun kirki, amma ba za ka so a ce ya zama saka rai ba. Sannan, aure, makaranta yana iya kai yara ko'ina, idan ba su iya kare kansu ba, ta yaya hankalin iyaye zai iya kwanciya?
Bugu da kari, Hauwa ta ce, idan yaro bai rama ba idan an ci zalinsa, ta yaya zai je ya fahimci rayuwa da mu'amala a wasu wurare yadda zai fahimci abun da duniya take ciki? Saboda ya kasance mai rauni. Sabo da haka, dole yaro ya kare kansa kafin ya kai kara domin hana faruwar hakan a gaba. Yaro zai iya kare kansa domin wasu yaran ko an kai karansu wajen iyaye ko malamai ba sa dainawa, kuma da zarar sun fahimci ana tsoronsu shi ne suke ci gaba.
Amma, malam Yahaya Babs bai yarda da yaro ya rama ba idan an ci zalinsa. Ya ce, ya kamata yaro ya kai kara a gaban iyaya ko malamai.
Malam Yahaya yana ganin cewa, yaron da yake cin zalin yara idan a kai bincike kila matashiya ne daga inda ya fito. Kuma watakila abun da ke faruwa ne a gidansu ya kawo yake cin zalin yara a makaranta. A waje daya, yana da kyau yaro ya kai kara, idan har aka ce an ci zalin yaro a ba shi yara ma akwai illah. Sannan idan har aka ce ya je yara ma shi ma zai koyo yadda ake cin zalin. Bugu da kari, idan a karfafa wa yara su rama, wallahi, zai karfafawa yaro yadda zai koyi yadda ake cin zalin.