logo

HAUSA

Hira da Mustapha Adam Usman dake karatu a kwalejin koyon likitanci ta Shenyang

2020-02-19 11:24:51 CRI

Hira da Mustapha Adam Usman dake karatu a kwalejin koyon likitanci ta Shenyang

A cikin shirinmu na wannan mako, wakilinmu Murtala Zhang ya zanta da Mustapha Adam Usman, wani dalibi dan jihar Jigawar Najeriya, wanda a yanzu haka yake karatun digiri na farko a kwalejin koyon ilimin likitanci ta Shenyang, dake lardin Liaoning na kasar Sin, wato Shenyang Medical College.

A zantawar tasu, Mustapha Adam ya bayyana fahimtarsa game da yakin da gwamnatin kasar Sin ke yi, na dakile yaduwar cutar numfashi ta coronavirus, ya kuma ce, ma'aikatan jinya na kasar Sin da suke aiki tukuru wajen kulawa da masu dauke da cutar, tamkar abun koyi na gare shi. Yana fatan kara bada gudummawarsa ga harkokin kiwon lafiya na kasarsa wato Najeriya, idan ya kammala karatun likitanci a nan kasar Sin.(Murtala Zhang)