logo

HAUSA

Mata Sinawa masu ba da gudummawar yaki da cutar Corona

2020-02-18 17:14:16 CRI

Yanzu kasar Sin na fama da annobar cutar numfashi ta coronavirus yanzu. Don haka a cikin shirinmu na yau, zan gabatar muku da wasu mata Sinawa da ke bayar da gudummawarsu a yayin da ake kokarin yakar cutar. Du Fujia, ma'aikaciyar jinya ce wato Nas, wadda ta shiga aikin yaki da cutar Corona bisa radin kanta, a asibitin jama'a na Meitan dake lardin Guizhou, kuma tun da ta shiga wannan aiki, ba ta samu hutu ba. Asibitin na daga cikin asibitoci 183 da aka ware domin kula da masu cutar Corona a lardin Guizhou. Tana kuma daga cikin kashin farko na ma'aikatan lafiya da suka shiga aikin yaki da cutar bisa radin kansu, a sibitin. Kididdiga ta nuna cewa, kawo yanzu, Kwayar cutar, wadda ta fara bulla a Wuhan na lardin Hubei, ta kama mutane fiye da 57,416 tare da sanadin mutuwar wasu sama da 1,665 a fadin kasar. A lardin Guizhou, an samu mutane 144 da aka tabbatar sun kamu da cutar, inda mutum guda ya mutu. A cewar Du, " kamar yadda dan uwana yake yaki a fagen daga, ni ma haka asibitin ya kasance min fagen daga yayin da ake tsaka da kokarin dakile yaduwar cutar Corona. Aikin kowanne likita da nas, shi ne kula da marasa lafiya, kuma mun shirya hidimtawa kasa". Dan uwanta, Du Fuguo, ya rasa hannaye da idanunsa lokacin da wani bam ya tashi yayin da suke aikin kawar da nakiyoyi a watan Okatoban 2018. Rundunar soji ta karrama shi a matsayin kwarzon soja a watan Yulin da ya gabata. "ina alfahari da shi, ya karfafa min gwiwa da irin kwarin gwiwarsa" cewar Du Fujia. "wannan ne bikin bazara na farko da dan uwana ya kasance a gida cikin shekaru 7 da suka gabata, amma ba zan iya kasancewa da shi ba, saboda kada in kai cutar gida", cewar Du Fujia.

Mata Sinawa masu ba da gudummawar yaki da cutar Corona

Ta nuna sha'awarta na shiga ayarin masu yaki da cutar Corona a asibitin nan take, bayan an sanar da wani shiri dake neman ma'ikatan lafiya su yi aiki a asibitin na kula da zazzabi, a ranar 27 ga watan jiya.

"nan take na amince ba tare da sanar da iyayena ba. Na san za su goyi bayan shirin", cewar Du Fujia. Ta ce duk da ba a samu wanda ya kamu da cutar a Meitan ba, mutane da dama sun ziyarci asibitin. Baya ga daukar yanayin zafin jikin mutane, Du Fujian na kuma nunawa mutane yadda za su kare kansu daga kamuwa da cutar da taimakawa wajen kwantar musu da hankali. Baya ga Du Fuguo da Du Fujia, akwai kuma wasu 'yan uwansu biyu, wato Du Fuqiang, soja dake aiki a bakin iyaka a yankin Tibet mai cin gashin kansa na kasar Sin, da kuma Du Fumin, likita a sashen kula da marasa lafiya masu tsanani a asibitin Meitan Jiali. "cutar ta bulla cikin gaggawa ba tare da an yi zatonta ba. Ya kamata ko wane Basine ya taimaka wajen yaki da cutar," cewar Du Fumin. Ya ce "ina fatan za a ci nasara kan wannan yaki da ba na bindiga ba" Du Fuguo na goyon bayan shawarar da 'yan uwansa suka yanke. "aikinsu ne ceton marasa lafiya. Kuma sun jajirce wajen aiwatar da shi," a cewar Du Fuguo, yana mai cewa, likitoci da sojojin dake aikin yaki da cutar Corona kwaraza ne a zukatanmu. Ya kuma yi kira da cewa, "kada gwiwarku ta yi sanyi, jami'an lafiya! Ku kasance masu kwarin gwiwa a Wuhan! Ku kasance masu kwarin gwiwa, Sinawa!" Labarinsu ya shahara a kafar intanet, mutane sama da miliyan 130 ne suka kalli labarin a shafin sada zumunta na Weibo. Har wani ya yi tsokaci cewa: "na jinjinawa mahaifiyarsu. Yaranta sun zama abun alfahari ga kasa". Kamar Du Fujia, akwai dubban likitoci da nas nas da suka jajirce wajen yaki da cutar Corona. A lokaci guda kuma, ana tura kusan dubu 30 jami'an lafiya daga fadin kasar Sin domin yaki da cutar a Hubei, wanda ya kebe kansa a wani kokari na dakile yaduwar cutar.

Mata Sinawa masu ba da gudummawar yaki da cutar Corona

Ma Jianjun ya wallafa wani sako a shafinsa na WeChat a ranar 26, rana ta biyu na bikin bazara na sabuwar shekarar Sinawa, domin karfafawa matarsa Jiang Xue gwiwa.

Jiang, shugabar nas a asibitin Tangdu, na rundunar sojin sama na Jami'ar nazarin aikin likita dake birnin Xi'an, na lardin Shaanxi na arewa maso yammacin kasar Sin, na aiki a wani asibiti domin kula da marasa lafiyar da suka kamu da cutar Corona a Wuhan, babban birnin lardin Hubei. Ganin kalaman kwarin gwiwa daga mijinta, ya sa Jiang zub da hawaye, kuma ta ce tana jin dadin goyon bayan da iyalinta ke ci gaba da ba ta, tana cewa a matsayinta na soja, za ta sauke nauyin dake wuyanta. Jiang na daya daga cikin jami'an lafiya da rundunar sojin kasar Sin ta aike domin kula da marasa lafiya a Wuhan. Bayan ganawar da ta yi da iyalinta cikin hanzari da safiyar ranar 24, jajibirin sabuwar shekarar Sinawa, Jiang ta koma asibiti, sannan ta wuce Wuhan da yamma tare da sauran takwarorinta. Sun isa filin jirgin saman birnin da tsakar dare. Kuma ba tare da sun hutu ba, dukkan jami'an suka fara aikin jinya da taimakawa likitoci a asibiti. Sai da Jiang da sauran takwarorinta suka tattauna kan yadda za su tunkari cutar kafin su fara ayyukansu na yin allura da rubuta bayanai da kula da marasa lafiya. Wasu daga cikin marasa lafiyar na cikin damuwa. Ko da yaushe, Jiang kan karfafa musu gwiwa domin saukaka fargabar da suke ciki. "kar ku damu. Muna tare da ku. Karfin imani zai sa ku ci galaba kan cutar" haka take fadawa marasa lafiya.

Mata Sinawa masu ba da gudummawar yaki da cutar Corona

Wannan ne karo na 3 da take gudanar da irin wannan muhimmin aiki, bayan iftila'in girgizar kasa ta Wenchuan na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin a shekarar 2008 da kuma tawagar agaji da aka tura ketare domin yaki da cutar Ebola a kasar Liberia dake nahiyar Afrika.

"Na yi muhimman ayyuka har sau 3 daga 2008 zuwa 2020. An gama 2, yanzu kuma dayan na gudana. Zan kammala aikin, kuma girmmawa ce ga rayuwata," a cewar Jiang.

Mata Sinawa masu ba da gudummawar yaki da cutar Corona

Saurin kammala ginin asibitin Huoshenshan cikin kwanaki 10, ya ba mutane mamaki. Asibitin mai fadin muraba'in mita 33,900 na dauke da gadaje 1,000 da kwararrun ma'aikatan lafiya 1,400.

Sama da masu amfani da kafar intanet miliyan 10 ne suka shaida kammaluwar aikin a ranar 2 ga watan Fabrairu a Wuhan, babban birnin lardin Hubei, kuma inda cutar Corona ta samo asali. Ma'aikata sama da 6,000 ne suka yi aikin ginin asibitin, inda suke aikin karba-karba sau biyu a rana, da nufin gaggauta kawar da cutar Corona. Daga cikinsu, akwai ayarin mata ma'aikata da ba su sadu da iyalansu ba yayin hutun bikin bazara domin wannan aiki, lamarin da ya ja hankalin duniya, a yayin da suke bada gudunmuwarsu ga yaki da cutar Corona. Mei Jun ta shirya komawa garinsu dake lardin Shandong na gabashin kasar Sin kafin ta samu labarin aikin ginin sabon asibitin a ranar 24 ga watan Janairu. Ta mayar da hankali wajen karbo kayayyaki da shirya motocin da za su yi aiki bayan an sanar da ita dangane da aikin. Ta kan yi ta aiki kan waya tsawon sa'o'i 6 a rana ba tare da hutawa ba ko da na shan ruwa ne. Sun Yanfang, wadda ke tsara abubuwan da ake bukata a kullum da kuma tsara matakan kare kai daga cutar a wajen da ake aikin, ta yi jarumtar komawa Wuhan daga garinsu na Shantou, dake lardin Gangzhou. Sai da ta yi tafiyar mota na tsawon sa'o'i 16 kafin komawa Wuhan. Sun da sauran 'yan tawagarta na sabunta makarin fuskar magina duk bayan sa'o'i 4, sannan suna feshin kwayoyin cuta a wajen, da ofisoshi da unguwanni a kullum. Kula da lafiya da abincin magina su ne abubuwan da ta fi ba muhimmanci.

Mata Sinawa masu ba da gudummawar yaki da cutar Corona

Hu Jusheng, ita ce mai kula da kayayyakin aiki. Duk da cewa tana kan hanyarta ne na zuwa garinsu a lardin Anhui na gabashin kasar Sin daga Wuhan, haka ta juya ta koma bayan an sanar da ita akwai aikin gaggawa na kula da kayayyaki. Ta shiga aikin ne nan take bayan tafiyar sa'o'i.

Wang Xiaohang, na daga cikin masu aikin samar da karafan ginin. Matar mai shekaru 53 ta shafe shekaru sama da 30 tana aiki a kamfanin, don haka kasancewarta a wajen aikin ya karfafa gwiwar sauran abokan aikinta. Wang ce ta dauki gabarar tsara duk wani bangare na aikin, ciki har da zane da kayayyaki da sauransu. Fan Wei, kwarrariyar mai zane, ita ce nauyin tuntubar masu zanen ginin ya rataya a wuyanta da hada kan ma'aikata domin tsara zane. Tana yawan zirga zirga tsakanin kamfanonin masu zane, da cibiyar dake jagorantar aikin da kuma wurin ginin. Ba ta baccin da ya zarce sa'o'i 4 a rana. Zhang Fen, ta ayarin masu samar da abubuwan da ake bukata a wajen ginin, ta kamu da mura mai tsanani kafin ta fara aikin. Duk da mijinta ya ba ta shawarar hutawa yayin hutun bikin bazara, Zhang ba ta karbi shawarar ba, inda ta amince da yin aikin bayan ta samu labari. Cikin kwanaki 10n, Zhang ta yi aikin sama da sa'o'i 12 a rana, na samar da kwangila da tsara yadda za a biya masu samar da kayayyaki.

Mata Sinawa masu ba da gudummawar yaki da cutar Corona

Han Jianyin, wadda ke aikin daukar ma'aikatan aiki, kan yi waya kimanin sau 80 a kowacce rana. An samu karancin leburori da kayayyakin gini a karshen shekara saboda bikin bazara.

Han ta fahimci fargabar maginan, don haka ta yi ta musu bayanin yanayin ta waya. "abun da ake bukata in yi shi ne samar musu da dukkan abun da ake bukata domin taimakawa ma'aikatan zuwa aiki-ko da kuwa zan je ne in dauko su daya bayan daya, to zan yi". Cewar Han.

Mata Sinawa masu ba da gudummawar yaki da cutar Corona

Yang Ning, shugabar masu kai kayyakin aiki, ta fara tattara motocin kai kayayyaki ne nan take bayan an sanar da ita game da aikin, domin ta san motocin sufuri su ne za su tabbatar da samar da kayyyakin da ake bukata.

Pan Yanjun, daya daga cikin ayarin masu bada taimako, na ta aikin shirya wajen ginin, da tura kayayyaki da tsara wajen kwana da sufurin ma'aikata. Tana bukatar buga waya sosai a kowacce rana. Duk da ba ta baccin da ya haura sa'o'i 5 a rana, ba ta taba kashe wayarta ba, don ko za a samu wata bukata ta gaggawa yayin da ake aikin. (Kande Gao)