shin aure tsakanin kasa da kasa yana da fa'ida?
2020-02-13 09:17:31 CRI
A cikin wannan sabon shiri na Duniyarmu A Yau, baki wadanda suka halarci tattaunawa sun yi musayar ra'ayoyinsu kan batun ko "shin aure tsakanin kasa da kasa yana da fa'ida?" inda Aliyu UbaTaura da Niimatullah suka yi musayar ra'ayoyinsu sosai.
A ganin Aliyu, yanzu akwai al'adu na kai lefe da sauransu, an ga akwai daman samun sauki idan wani bangaren na aura. Kamar yanzu shi baki ya auri Baturiya, zai haifi yara masu kyaun gani. Kuma za a iya fahimtar bambancin al'adu.
Sannan kuma ana da daman dan wata kasa. Bugu da kari, a ganin Aliyu, banbancin al'ada zai sa a samu chanjin da ake bukata wajen zamantakewar auratayya.
Amma Ni'imatullah ba ta amince da aure tsakanin kasa da kasa ba. Tana ganin cewa, aure tsakanin kasa da kasa zai iya kawo kalubale, kuma aure ba abun wasa ba ne, akwai iyali, ba mutane biyu kadai ba ne akwai iyaye da 'yan uwa.
Sannan abincin dake tsakanin kasashe daban daban ma ya banbanta, yarensu ma ya banbanta. Sabo da haka, tabbas ne akwai matsala wajen zama, da yanayin rayuwa. Kuma za a iya tabbatar da ganin an samu fahimtar juna tsakanin iyalan ma'aurata biyu?