logo

HAUSA

Matan dake taka rawa wajen yaki da cutar numfashi

2020-02-11 15:18:12 CRI

Kamar yadda aka sani, yanzu kasar Sin na fama da yaduwar cutar numfashi.

Game da cutar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, yayin da ake kokarin tinkarar cutar numfashi da ta bullo a kasar, ya kamata dukkan sassan kasar su zama karkashin jagorancin kwamitin tsakiya na jami'iyar Kwaminis ta kasar Sin, inda za a mai da tsaron rayukan jama'a da lafiyarsu a gaban kome. Za a dauki matakai daga bangarorin doka, da aiwatar da su, da kokarin martaba su, ta yadda za a kyautata dabarun hana yaduwar cuta, da daidaita al'amura bisa doka, don tabbatar da gudanar aikin dakile cutar yadda ya kamata.  

Matan dake taka rawa wajen yaki da cutar numfashi

 

Yanzu, dukkan al'ummar kasar Sin na kara hada kansu kamar yadda su kan yi a yayin da suke tinkarar manyan matsalolin dake gabansu. Wadanda suka cancanci a yaba musu su ne likitoci da masu aikin jinya. Yanzu bari mu saurari labaran wasu daga cikinsu.

Hu Xuejun, nas ce dake aiki a wani asibiti dake birnin Wuhan, birnin da wannan cuta ta bulla a kasar, ya zuwa yanzu tana aikin yaki da cutar har na tsawon wata guda. Ta gaya mana cewa, a yayin da ta samu labari cewa, akwai wadanda suka kamu da cutar da suka warke, har ma an sallame su daga asibiti, wannan shi ne abun da ya fi faranta mata rai. Ta gaya wa wakilinmu cewa, yanzu akwai masu aikin jinya da suka fito daga wasu asibitoci wadanda suka zo asibitinsu don nuna goyon baya, hakan ya rage musu aiki sosai, suna iya samun lokaci don su dan huta, tana cike da imanin cewa, za a samu kyautatuwar yanyin da ake ciki yadda ya kamata.  

Matan dake taka rawa wajen yaki da cutar numfashi

 

Masu sauraro, sanin kowa ne cewa, masu aikin jinya suna daga cikin rukunin da ya fi fuskantar hadarin kamuwa da cutar, saboda suna mu'ammala da wadanda suka kamu da cutar sosai. Guo Qin, yar shekaru 38 a duniya, nas ce dake aiki a cibiyar ceto ta gaggawa ta wani asibitin dake birnin Wuhan, a ranar 13 ga watan Janairu, aka tabbatar ta kamu da cutar numfashin , bayan an kebe ana kuma ba ta kulawa, a ranar 28 ga wata ta warka daga cutar, a safiyar wannan rana kuma, sai ta koma cibiyar ceto ta gaggawa don ci gaba da kula da wadanda suka kamu da cutar. Kana ta kan bayyana wa wadanda suka kamu da cutar yadda ta warke daga cutar, ta gaya musu cewa, cutar ba abu ne mai ban tsoro ba, kai kamata a damu ba. Guo Qin ta gayawa wakilinmu cewa, abokan aikinta suna ta sun dauki lokaci mai tsawo suna gudanar da aiki, dukkansu sun gaji sosai, za ta komo wajen aikinta bayan ta warka, don ta ci gaba da aiki yadda ya kamata. A cewarta, "Ni 'yar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ce, ya kamata na taka rawar ba da jagoranci a yayin da ake yaki da cutar numfashin."

A nata bangaren, Bai Hui, 'yar shekaru 32 a duniya, ita ma na aiki ne a wannan asibitin, ta gaya mana cewa, "Da na ji an ce, na kamu da cutar, sai hawaye ya zubo min, da farko na ji tsoro sosai, amma sakamakon kwarin gwiwa da abokai na suka ba ni, hankali na ya kwanta sannu a hankali." Bayan kwanaki kimanin goma sai Bai Hui ta warke aka kuma sallame ta daga asibitin. Ta ce, yanzu ta sake komowa aikinta, tana kuma cike da imani na cimma nasarar yaki da cutar a nan kasar Sin.