An daga lokacin gudanar da gasar CFA Super Cup sakamakon bullar cutar coronavirus
2020-02-07 10:06:32 CRI
Hukumar kwallon kafar kasar Sin CFA, ta sanar da dage lokacin gudanar da gasar manyan kulaflikan kasar Sin ko "Super Cup" da ake gudanarwa a duk shekara, wadda kuma kafin dage lokacin gudanar da ita, an shirya bude gasar ne a ranar 5 ga watan nan na Fabarairu a birnin Suzhou, na lardin Jiangsu. Sanarwar da hukumar kwallon kafar kasar Sin CFA ta fitar cikin karshen makon jiya, ta ce matakin dage gasar ta shekarar 2020 din nan, yana da nasaba da yunkurin da ake yi na kandagarki, da kuma matakan dakile yaduwar cutar numfashin da ke kara bazuwa a sassan kasar, wanda daya daga matakan hakan shi ne kaucewa taruwar mutane da yawa a wuri guda. Sanarwar ta kara da cewa, nan gaba hukumar ta CFA za ta sanar da lokacin da za a gudanar da gasar ta Super Cup.
An dai samu bullar cutar corona virus ne a karon farko a birnin Wuhan na tsakiyar kasar Sin, kuma cikin kankanen lokaci cutar ta bazu zuwa sauran sassan kasar. Ya zuwa karshen ranar Juma'ar makon jiya, adadin wadanda cutar ta hallaka sun kai 41, an kuma tabbatar da kamuwar Karin mutane 1,287 a yankunan lardunan kasar 30. (Saminu Alhassan)