Shin ya kamata a nunawa yara yadda ake sana'a ko sai sun gama makaranta?
2020-01-30 14:22:37 CRI
A cikin wannan sabon shiri na Duniyarmu A Yau, baki wadanda suka halarci tattaunawa sun yi musayar ra'ayoyinsu kan batun "shin ya kamata a nunawa yara yadda ake sana'a ko sai sun gama makaranta?" inda malama Ni'imatullah da Hajiya Hauwa Ibrahim Bello suka yi musayar ra'ayoyinsu sosai.
A ganin Ni'imatullah, ya kamata a nunawa yara yadda ake sana'a a lokacin da suke makaranta. Sabo da, yanzu zamanin da muka saka kanmu shi ne akwai karancin aiki, kuma an ce, ilmi shi ne gishirin zaman duniya, sai awayi gari an gama makaranta ba aikin yi.
Bugu da kari, tun yaro yana karami, amma ya kamata a gwada masa sana'a. Bai kamata a tura yaro makaranta kawai ba tare da nuna masa aikin hannu ba.
A ganin Hauwa Ibrahim Bello, babu bukata a nuna wa yara yadda ake sana'a a lokacin da suke karatu a makanra. Sabo da a cikin ilimin da yara suka koya da shi zai tashi wata rana suka koyi sana'a.
Sannan, a makaranta, ana so a koyawa yara ilimi ne da fasaha, ba tare da nauyin wata sana'a ba. Bugu da kari, sana'a dabam ilimi daban, ilimi shi ne gaba da sana'a. Saboda idan aka ce a koyawa yara sana'a a makaranta, karatun na ba zai yi ba. (Ibrahim, Fatimah, Hauwa, Ni'imatullah)