logo

HAUSA

Shin kudin iyalinka naka ne ko ba naka ba?

2020-01-23 08:52:40 CRI

A cikin wannan sabon shiri na Duniyarmu A Yau, baki wadanda suka halarci tattaunawa sun yi musayar ra'ayoyinsu kan batun "Shin kudin iyalinka naka ne ko ba naka ba?", inda Hajiya Hauwa Ibrahim Bello da malam Yahaya Babs suka yi musayar ra'ayoyinsu sosai.

Shin kudin iyalinka naka ne ko ba naka ba?

A ganin Hauwa, idan har mace tana nema tana samu, wanda take tare da shi zai iya mata abun da take so da kudinsa tabbas abun da ta mallaka ya zama nashi shi ma. Bugu da kari, idan akwai so da kauna da fahimtar juna babu daman da ya nuna cewa a yi wa juna munafurci a kan abun duniya.

Sannan Hajiya Hauwa ta ce, mijinta zai iya amfani da kudinta wajen tallafin sauran iyalansa saboda fahimtar juna. Daga karshe dai, Hauwa ta bayyana cewa, tana da iko da daman amfani da kudin mijinta, shi ma yana da daman yin hakan da nata.

Shin kudin iyalinka naka ne ko ba naka ba?

Amma malam Yahaya Babs bai amince da ra'ayin Hauwa ba. Ya ce, kudin mai dakinsa wato matarsa ba nasa ba ne. Watakila ban da shi ko yana da bukata zai iya tambayar ta. Sannan matarsa tana iya taimaka masa a matsayinsu na ma'aurata amma sigar ba ta chanja ba kudinta ne. Bugu da kari, a kaddara namijin ya fadi ya mutu kudin nan ya zama kayan gado.

Daga karshe dai, malam Babs yana kuma ganin cewa, mai dakinsa za ta iya taimaka masa idan ba shi da aikin yi saboda aurensu ko soyayya amma kudinta ne ba nasa ba. (Ibrahim, Fatimah, Hauwa, Yahaya Babs)