logo

HAUSA

Aguero Ya Karya Tarihin Henry Da Alan Shearer

2020-01-22 09:24:30 CRI

Na Bawa Morata Hakuri, Cewar ValverdePublished

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Fede Valverde, ya bayyana cewa baiji dadin abinda ya yiwa Albaro Morata ba sai dai yace bazai iya komai ba a lokacin sai dai yayi masa keta amma kuma daga baya ya bashi hakuri. Real Madrid ta lashe kofin Spanish Super Cup, bayan da ta yi nasara a kan bokiyar hamayyarta, Atletico Madrid a bugun fenariti ranar Lahadi bayan da kungiyoyin suka tashi wasan 0-0, hakan ya sa aka kara musu minti 30, amma ba a samu gwani ba a fafatawar da suka yi a Saudi Arabia. Real Madrid ta kare gumurzun na hamayya da 'yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Federeico Valberde jan kati bayan da dan wasan ya yi wa Alvaro Morata keta a minti na 116 da wasan, dalilin da ya sa alkalin wasa Jose Maria Sanchez Martinez ya bashi jan kati. "Tabbas abinda nayi banyi dai-dai ba saboda ba abinda yakamata nayi ba kenan sai dai nayi duk iya abinda zanyi domin ganin na dakatar dashi amma ban samu ba saboda haka na yanke hukuncin yi masa keta" in Valverde Ya kara da cewa "Banji dadin abinda nayiwa Morata ba saboda dan wasa ne wanda bashi da mugunta kuma tsohon dan wasan wannan kungiya amma kuma bayan an tashi naje na bashi hakuri saboda abinda nayi masa"

Bayan da lokaci ya cika aka je bugun fanareti Real ta yi nasara da ci 4-1 sannan Real Madrid tana ta biyu a teburin La Liga da maki iri daya da na Barcelona wadda take ta daya a teburin gasar bana sannan Real Madrid ta kai wasan karshe ne, bayan da ta doke Valencia daci 3-1, ita kuwa Atletico Barcelona ta ci 3-2.

Aguero Ya Karya Tarihin Henry Da Alan Shearer

Dan wasan gana na kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Sergio Aguero, dan kasar Argentina, ya ci kwallo uku rigis kuma karo na 12, ya kuma kafa tarihin bakon dan wasa wanda ba dan kasar Ingila ba da yake kan gaba a cin kwallo a firimiya.

A ranar Lahadi Manchester City ta doke Aston Villa da ci 6-1 a wasan mako na 22 a gasar Premier a filin wasa na Villa Park kuma kwallayen da Aguero ya ci ya haura na tsohon dan wasan Arsenal, Thierry Henry, ya kuma yi kan-kan-kan da kwallo 177 da Frank Lampard ya zura a raga a gasar firimiya. Wadanda ke gaban Aguero kawo yanzu sun hada da Alan Shearer da Wayne Rooney da kuma Andy Cole, amma shi ne kan gaba a yawan cin kwallaye uku rigis a inda kawo yanzu yaci kwallaye uku sau 12 a tarihi. Wannan ne wasa mafi muni da magoya bayan Aston Villa suka gani, bayan wanda Liberpool ta yi musa 6-0 a Villa Park a Fabrairun shekara ta 2016 wanda sakamakon yasa magoya bayan kungiyar suka dinga fita tun kafin a tashi. Riyad Mahrez ne ya ci kwallo biyu a wasan da wadda Gebriel Jesus ya ci da kuma Aguero da ya ci uku rigis a raga sannan Manchester City ta dawo ta biyu a kan teburi, amma da tazarar maki 14 tsakaninta da Liberpool mai jan ragamar teburin firimiya na bana kuma da kwantan wasa daya. Bayan tashi daga wasan ne kociyan Manchester City, Pep Guardiola ya bayyana cewa dan wasa Aguiro yana da abin mamaki kuma ya kafa tarihi a kungiyar wanda za'a dade kafin a samu wanda zia karya wannan tarihin. Daga matsayin Bayern Munich zuwa sabon mataki karkashin jagorancin Oliver Kahn

Zaman Oliver Kahn kan kujerar ofis ta kasance takaitacciya matuka, domin kuwa jim kadan da gabatar da shi a matsayin jagoran horaswa na kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich, a dakin taron kungiyar, sai tsohon mai tsaron gidan da a yanzu ke da shekaru 50 da haihuwa ya shiga tawagar kungiyar, zuwa birnin Doha, inda Bayern Munich din za ta yi atisayen lokacin hunturu. Masharhanta da dama dai na ganin zuwa Kahn a wannan gaba, zai iya share sabon fage a tarihin nasarorin kungiyar. kahn wanda da shi aka lashe gasar zakarun turai ta shekarar 2001, ya kulla kwangilar shekaru 5 da Bayern, irin kwangilar da magabacin sa Karl-Heinz Rummenigge ya kulla da kungiyar zuwa karshen shekarar 2021. Kafin nan ana ganin Kahn zai kasance muhimmin jigo a wannan kungiya. A gefe guda, sabon kocin wanda a baya ya taba lashe lambar yabo ta dan wasa mafi hazaka har karo 3, ya kasance cikin tawagar da ta lashe gasar cin kofin kasashen turai na shekarar 1996, ya kuma jima ana dama wa da shi a harkar tsare tsaren kungiyar. Da yake tsokaci yayin kama aiki, Kahn ya ce aikin sa ya wuce na maimaita tarihin nasarar kungiyar, domin kuwa burin sa shi ne, samar da Karin ci gaba ga kungiyar a dukkanin fannoni. Kahn ya ce yana fatan ci gaba da wanzar da akidun Bayern, wato matsayin ta na kungiya mai yanayi na iyali guda, wadda za ta ci gaba da tunkarar kalubalen da ke tafe a nan gaba. Sabon kocin wanda a baya ya bugawa kungiyar kasar Jamus kwallo, ya ce burin sa na kurkusa shi ne, lashe kofin kalubake na kasar a karo na 8, yayin kammala kakar wasanni ta wannan karo. Ya kuma bayyana burin sa na gaba, ciki hadda samar da 'yan wasa masu ilimi da basira da za su yi fice, da gina tsarin wasa mai nagarta, da samar da salon wasa mai dorewa na kungiyar. Ya ce lashe kofin zakarun turai shi ma yana da matukar muhimmanci. Ya ce "Tun asali babban burin wannan kungiya shi ne, kasance a sahun gaba a dukkanin gasanni," "Bayan shekaru 14 da rigar Bayern, ni ma wannan ya riga ya zama akida ta. Sakamakon Karfin Hali Masu kallon yanayin kungiyar, na ganin bayan kasancewar Kahn kyaftin din kungiyar tsawo kusan shekaru 10, a yanzu zai koma kungiyar da karfin zuciyar cimma nasarori. Shi da kan sa ya bayyana cewa, 'yan kwanakin da suka gabata, sun sa zuciyar sa ta cika da shaukin aikin dake gaban sa. Kahn ya kara da cewa, abu ne mai wahala mutum ya iya barin wannan kungiya, saboda banbancin ta da sauran kungiyoyin kwallon kafa. Kuma da ma kokarin kara kyautata kwarewa, da cimma karin nasarori daya ne daga muhimman burikan masu tara leda a matsayi na kwarewa. Ya ce hakan ne ma taken kungiyar Bayern. Kuma shi ma halin sa shi ne rashin yanke tsammani na duk wata nasara. Kahn ya ce yana fatan nan gaba zai yi sanyi, kasancewar an fi sanin sa da halayyar zafin zuciya. Shugaba mai hikima Oliver Kahn ya ce za a bude kofar kungiyar Bayern ga dukkanin 'yan wasa, domin kuwa hakan ne ya mayar da kungiyar mafi kwarewa a duk duniya. Za a lura da yanayin halayyar 'yan wasa, domin sanin matakan dauka a duk lokacin da ake taka leda, ya ce Bayern kungiya ce mai lura da yanayin bil Adama. Yanzu dai babban aikin Kahn shi ne daidaita yanayin karbar aiki daga Rummenigge, domin kafa sabon ginshikin wasa ga kungiyar. Kahn ya jima yana aiki sannu a hankali, domin tabbatar da sauyin sa, bai haifar da wata matsalar ta daban ba. Daga yanzu kuma, zai rika kara shigar da salon sa sannu a hankali cikin tsarin gudanar da wasannin kungiyar. Ana sa ran zai yi aiki cikin hadin gwiwa da manyan masu fada a ji na Bayern, da suka hada da jagoran ta Herbert Hainer, da Rummenigge, da daraktan wasanni Hasan Salihamidzic. Batun mai tsaron gida Batun kulla kwangila tsakanin Bayern da mai tsaron gidan Schalke Alexander Nuebel na jawo cece kuce, a gabar da matashin golan mai shekaru 23 da haihuwa, ya sanya hannu kan kwangilar shekaru 5 da Bayern, tun daga lokacin bazarar shekarar nan ta 2020. An ce Nuebel na fatan zai doke matsayin bajintar Manuel Neuer, wanda shi ne babban mai tsaron ragar kungiyar. A daya hannun, Neuer wanda ke rike da lambar yabo ta dan wasa mafi kwarewa na shekarar 2014, kuma wanda sau hudu yana karbar lambar bajinta ta duniya ta gola mafi kwarewa, ya nuna rashin yarda da samar da gurbi ga Nuebel cikin wasanni 15 da kungiyar za ta buga. Neuer dai tuni ya fara nazari game da tsawaita kwantiragin sa da kungiyar zuwa shekarar 2023. Kahn dai na da ra'ayin cewa, dole ne kungiyar ta dauki Nuebel, kasancewar sa lamba daya cikin matasan yan wasa da ake alfahari da su a Jamus, amma kuma a cewar sa, Neuer ne zai ci gaba da zama babban golan kungiyar. Ya ma kira yunkurin dauko Nuebel a matsayin babban kwazo. Ya ce dukkanin masu ruwa da tsaki sun amince da shigowar Nuebel kungiyar, kasancewar sa matashi da zai iya yin koyi da lamba daya na duniya wato Neuer, da ma takwaransa enqueue. Kahn ya ce "Dole mu mayar da hankali ga zango na biyu na kakar wasan bana kafin komowa ga wancan batu a lokaci mafi dacewa, zan kuma ci gaba da tuntubar abokan aiki domin shawo kan wannan matsala". Fatan kungiyar Jagoran kungiyar ta Bayern Herbert Hainer, ya yabi kwarewar Kahn, kasancewar sa dan kwallo mai basira, dan kasuwa, kuma jagora na gari. Ya ce zuwan sa a matsayin mai horaswa zai baiwa kungiyar damar ci gaba da buga kwallo, irin wadda magoya baya zasu yi sha'awa, karkashin tsarin tattalin arziki mai daraja, kuma wanda zai samu karbuwa a dukkanin bangarori. A bangaran sa, Kahn ya ce "Akwai bukatar mu yi amfani da dukkanin damar mu ta jami'ai da muke da su, don samar da kofar karbar shawarwari mabanbanta, don gano bakin zaren matsalolin mu, ni kai na abokin hulda ne ga kowa, za kuma mu yi aiki tare".

Daga karshe ya ce fatan sa shi ne kungiyar Bayern Munich ta zamo ta daya a dukkanin gasannin kasa da kasa. Ya ce "kungiyar mu da wasannin ta, su ne a gaban mu. Kuma dukkanin mu mun san cewa kaiwa matsayi na koli shi ne aikin mu a kullum."