logo

HAUSA

Hadin-gwiwar Sin da Afirka za ta amfani duk duniya a sabuwar shekara

2020-01-22 09:05:48 CRI

Hadin-gwiwar Sin da Afirka za ta amfani duk duniya a sabuwar shekara

A kwanakin baya ne wato a ranekun 7 zuwa 13 ga wata, memban majalissar gudanarwa, kana ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya ziyarci wasu kasashen Afirka biyar, ciki hadda Masar, Djibouti, Eritrea, Burundi, da kuma Zimbabwe. Ministan harkokin wajen kasar Sin ya kan zabi kasashen Afirka a matsayin ziyararsa ta farko a sabuwar shekara, a shekaru talatin da suka shige, al'amarin da ya zama al'ada a harkokin diflomasiyyar kasar Sin. Kamar yadda minista Wang Yi ya ce, kasar Sin ba ta taba sauya manufarta kan kasashen Afirka ba, ta kuma dade tana kulla zumunta, da zurfafa hadin-gwiwa tare da kasashen Afirka.

A shirinmu na wannan mako, wakilan sashin Hausa na CRI Ahmad Inuwa Fagam da Murtala Zhang za su tattauna kan ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kai a Afirka, tare da gabatar da sharhin da wasu jami'an gwamnati gami da masana dangantakar kasa da kasa na tarayyar Najeriya suka yi kan hadin-gwiwar dake tsakanin Sin da Najeriya da ma Afirka baki daya.(Murtala Zhang)