Malamai mata dake ba da gudummawa wajen cudanyar al'adun kasa da kasa
2020-01-20 21:01:43 CRI
Makarantar sakandare ta Bettina-von-Arnim-Schule, ita ce makarantar farko da ta mai da harshen Sinanci a matsayin harshen waje na biyu a Berlin, hedkwatar mulkin kasar Jamus. Madam Kathleen Wittek ita ce malama daya tak dake koyar da Sinanci a makarantar. Amma yanzu, yawan malamai masu koyar da Sinanci ya karu zuwa hudu. Madam Wittek ta bayyana cewa, "wani halin musamman na makarantarmu shi ne mun mai da Sinanci a matsayin harshen waje na biyu da darasin ba da ilmin al'adu. Wannan ya shaida cewa, ban da koyar da harshe, dalibai za su koyi ilmin da ya shafi kasar Sin, ciki har da halin da Sin ke ciki, kide-kidenta, abincinta, rubutunta da dai sauransu. Ban da wannan kuma, mun bai wa daliban damar zuwa kasar Sin don karo ilmi, ta yadda za su fahimci al'adun Sin daga dukkan fannoni."
Haka kuma Madam Wittek ta furta cewa, dalilin da ya sa makarantarta ta mai da hankali kan aikin koyar da Sinanci shi ne, na farko, koyon harshen waje zai taimaka wajen kyautata kwarewar dalibai a fannin cudanya a tsakanin al'adu daban daban, ganin yadda kimanin kaso 20 na al'umma ke mai da Sinanci a matsayin harshensu. Na biyu, sakamakon karuwar karfin kasa, Sin na taka muhimmiyar rawar a zo a gani a cikin harkokin duniya. Sin da Jamus na cudanya da hadin kai sosai, don haka koyon Sinanci zai bai wa dalibai damar samun guraben ayyukan yi a nan gaba.
Wittek ta fara mu'amala da kasar Sin ne tun tana karama, ta dade tana zaune a kasar tare da iyayenta, ta kuma zabi Sinanci a matsayin fannin da za ta yi nazari a kai a yayin da ta ke karatunta a jami'a, sa'an nan ta je birnin Nanjing na kasar don karo ilmi. Kawo yanzu dai, makarantar Bettina-von-Arnim-Schule da makarantun kasar Sin sun riga sun shirya harkokin hadin kai da cudanya da dama, Wittek kuwa ta kan ziyarci kasar Sin don rangadin aiki. A ganinta, a cikin shekaru fiye da goma da suka wuce, Sin ta samu babban ci gaba a fannoni daban daban, abin da ya fi burge ta shi ne yadda aka kyautata matsayin rayuwar jama'ar Sin. Wittek tana mai cewa, "har yanzu ina tuna yayin da nake karatu a kasar Sin a shekarun 1990 albashin malamai ba shi da yawa. Amma yanzu, malamai da dama sun shiga rukunin masu matsakaicin }arfi, wato suna da kudin sayen gida da mota, da ma zuwa ketare don yawon shakatarwa. Idan muka kwatanta da baya, lallai kasar Sin ta samu ci gaba a bayyane."
Bugu da kari, Wittek ta ce, a duk lokacin da ta zo kasar Sin, tana ga wasu sabbin canje-canje. Ban da ita ma, daliban da suka zo kasar Sin su ma sun kara fahimtar kasar, da ma sada dankon zumunci tare da dalibai Sinawa. Ta ce,
"A gani na, daliban da ke koyon Sinanci za su zama wani muhimmin bangare na sa kaimi ga cudanyar al'adun Sin da Jamus. Yanzu ana kara samun hanyoyin koyon Sinanci da ma kara fahimtar al'adun Sin, baya ga zuwa Sin bude ido. Ana shimfida gadojin cudanyar juna. Ni ma ina so in ci gaba da zama manzon musamman a tsakanin Sin da Jamus a fannonin harshe da al'ada, ta yadda dalibai masu yawa za su samu damar kusantar Sin da ma fahimtar kasar."
Wittek ta kuma yi bayanin cewa, daga shekarar 2007 zuwa yanzu, daliban da ke makarantar Bettina-von-Arnim-Schule na iya zabar darasin koyon Sinanci sau biyu a ko wane mako. A waje daya kuma, makarantar da dimbin makarantun sakandare na birnin Hangzhou da Beijing na raya dangantakar abuta ta hadin kai har na tsawon shekaru fiye da goma, wadanda ke da shirin musanyar dalibai a ko wace shekara.
Yanzu bari mu leka malama Do Thanh Van, da ke aikin koyarwa a kwalejin Confucius ta jami'ar Hanoi da ke kasar Vietnam.
An kafa kwalejin Confucius ta jami'ar Hanoi ne a watan Disamban shekarar 2014, bisa hadin gwiwar Jami'ar Hanoi ta kasar Vietnam da Jami'ar koyon aikin malanta ta Guangxi da ke kasar Sin, wadda ta kasance wani muhimmin sakamako na cudanyar ilmi da al'adu. Tun kafuwarta zuwa yanzu, Do Thanh Van, ta ke shugabar kwalejin bangaren Vietnam, wadda ta ganam ma idanunata ci gaban kwalejin sannu a hankali.
Do Thanh Van ta taba karatu a Jami'ar Fudan da ke birnin Shanghai har na tsawon shekaru uku, lamarin da ya sa ta hada kai da kwalejin Confucius. A shekarar 2008, ta taba zuwa kwalejojin Confucius da ke Thailand da Singapore don samun horo. Ta furta cewa, tun daga wancan lokaci, tana jiran a kafa kwalejin a kasarta ta Vietnam. Ya zuwa yanzu ma dai, an riga an kafa kwalejin a Vietnam tun shekaru biyar. Yayin da take waiwayar wadannan shekarun biyar, Do Thanh Van ta ce, kaddamar da wani aiki na da matukar wahala, sakamakon rashin fasahar kafa makaranta, sun sha wahala matuka da farko. Ta kara da cewa,
"Ba mu da isassun ma'aikata, aikin ya yi mun yawa, lallai mun sha wahalhalu. Amma irin sakamakon da muka samu, da ma gudummawar da muke bayarwa ga cudanyar al'adu, na gamsu sosai." Bisa kokarin dukkan malaman da ke kwalejin Confucius, makon nuna al'adun Sin, da gasar rera wakokin Sin, da koyon Sinanci cikin farin ciki, duk wadannan harkokin sun samu karbuwa sosai a wurin. Ban da wannan kuma kungiyar rera waka, da ta raye-raye, da ma ta wasan Kongfu da kwalejin ta kafa sun jawo hankulan dimbin dalibai. Do Thanh Van ta ce, in an kwantata da farkon kafuwar kwalejin, za a ga cewa, yanzu yawan daliban da ke kwalejin ya karu sosai, harkokin da ta shirya ma suna da yawa. Bayan da daliban kasar Vietnam suka fahimci kwalejin Confucius din, ba ma kawai sun nuna matukar sha'awa ga harkokin da kwalejin ta shirya ba, har ma da damansu su kan zo kwalejin don aikin sa kai. Ko da yaushe kwalejin na mai da hankali kan bukatun dalibai yayin da take raya ayyukan koyarwa, kafin ta shirya harkoki, ta kan yi bincike don fahimtar ra'ayin dalibai. Alal misali, kafin kafa kungiyar raye-raye, ra'ayoyin jama'a da aka tattara sun nuna cewa, daliban kasar Vietnam na sha'awar salon raye-rayen kasar Sin, hakan ya sa kungiyar ta jawo hankalin daliban da ba sa sashen koyon ilmin Sinanci bayan kafuwarta. Yanzu kungiyar da ta hada da dalibai daga jami'o'i daban daban kan nuna wasanni a wurare daban daban. Do Thanh Van tana mai cewa, "Yanzu kungiyar raye-rayen ta zama daya daga cikin kungiyoyi mafi shahara a kwalejin. Har ma a gun bukukuwan da jami'ar Hanoi ta shirya da ma harkokin cudanyar dalibai da birnin Hanoi ya shirya, a kan gayyaci kungiyarmu don nuna wasa, lallai kowa da kowa na alfahari da hakan."
Yanzu kwalejin Confucius ya zama wani muhimmin bangare na zaman daliban jami'ar Hanoi, abin da ke shaida cudanyar jami'ar da ketare. Kwalejin na tsara shirin na kara samun ci gaba a shekaru biyar masu zuwa, game da wannan, Do Thanh Van na cike da imani, da burin kaddamar da wasu ayyukan nazarin kimiyya tare da bangaren Sin. Do Thanh Van ta ce,
"Kwalejinmu na da shirin shirya wasu taruruwan kara wa juna sani a tsakanin Sin da Vietnam da tsakanin kasashen da ke kudu maso yammacin nahiyar Asiya. Ban da wannan kuma, za mu kafa kungiyar malamai masu koyar da Sinanci a kasar Vietnam ta farko, a kokarin tattara malamai da dama masu basira wajen samar da littattafan koyarwa da ke iya biyan bukatun daliban kasarmu, da ma tsara shirye-shiryen aikin koyarwa mafi dacewa ga dalibai a matakai daban daban."
Dalibai na ganin cewa, Do Thanh Van shugaba ce mai kirki, wadda ke son gudanar da ko wane aiki da kanta. Dalilin da ya sa daliban ke kaunarta shi ne sabo da ta shimfida wata gadar cudanya a tsakanin Sin da Vietnam.(Kande Gao)