Shin ya kamata a bar yara su shiga kafofin sada zumunci ko sai sun girma?
2020-01-16 08:32:12 CRI
A cikin wannan sabon shiri na Duniyarmu A Yau, baki wadanda suka halarci tattaunawa sun yi musayar ra'ayoyinsu kan batun "Shin ya kamata a bar yara su shiga kafofin sada zumunci ko sai sun girma?", inda Hajiya Hauwa Ibrahim Bello da malam Ali Uba Taura suka yi musayar ra'ayoyinsu sosai.
Hajiya Hauwa Bello ta ce, ya kamata a yarda da yara su yi amfani da shafin sada zumunta, ta yadda yara za su iya sanin hanyoyin yin mu'amala da sauran mutane a kan yanar gizo, da kuma za a iya kawowa yara dauki. Bugu da kari, iyayen yara za su iya saninhalin da yaransu ke ciki a yayin da suke wajen ayyuka. Sannan, a ganin Hauwa, shafin sada zumunta yana taimakon yara wajen koyon aikin makaranta.
Amma a ganin Ali Uba Taura, rashin taro ya yi yawa a shafin sada zumunta, sannan yara suna shiga kafan sada zumunta suna haduwa da azzalumai. Bugu da kari, shafin sada zumunta na dauke hankalin yara wajen karatu, har ma yana sawa yara koyon badala.