logo

HAUSA

Kabilar Du Long: Inganta nasarorin da aka cimma a fannin kawar da talauci ta hanyar yada al'adun kabila

2020-01-14 19:23:38 CRI

Kabilar Du Long: Inganta nasarorin da aka cimma a fannin kawar da talauci ta hanyar yada al'adun kabila

 

Kabilar Du Long karamar kabila ce da yawan al'ummarta bai kai 7000 ba a nan kasar Sin, 'yan kabilar suna zaune ne a kwazazzabon kogin Du Long dake kafar tsaunukan Hengduan na kasar Sin. Tsaunukan kankara ne masu yawa dake kewayen wurin, wanda kuma ake kiran shi "Yanki mai ban mamaki a kudu maso yammacin kasar".

A cikin dubu-duban shekarun da suka gabata, 'yan kabilar Du Long suna zaune a cikin gidajen da aka gina da haki, suna shuke-shuke ta hanyar da ake bi tun can can da, suna keta kogi ta hanyar igiya, kuma suna fita wajen wurin ne ta dogwayen tsani da aka yi kan dutse. Alal hakika babu cudanya ko kadan a tsakaninsu da na ketare, kuma sun yi fama da talauci sosai.

Amma, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, a karkashin goyon baya daga gwamnatin kasar Sin, an gina hanyar mota, da samar da wutar lantarki, da kafa tsarin sadarwa a garin Du Long Jiang, aka kuma samar da gidaje ga mazauna wurin, hakan ya sa aka soma yake-yaken fama da talauci. A shekarar 2018, duk 'yan kabilar Du Long sun cimma nasarar fita da talauci, ta yadda suka samu babban sauyi a zamantakewar al'umma a zamanin da da can, zuwa ta zamani, da ba a taba ganin irinta ba a tarihi, wadda ta shafi tsawon shekaru sama da dubu daya.

Al'adu muhimmin abu ne dake kiyaye rayuwar wata kabila, da kuma ci gabanta. Idan an yi fatan inganta nasarorin da 'yan kabilar suka cimma wajen kawar da talauci, da cimma burin samun wadata, akwai kuma bukatar a kara ba da ilmin al'adu mai salon musamman na kabilar, da kara karfin yada irin al'adun gargajiyar. Game da haka, shugaban makarantar garin mai tsarin hada kan firamare da sakandare mista Yang Siyang yana ganin cewa, ya kamata a soma kara wa 'yan kabilar imani kan al'adunsu tun daga lokacin yarintarsu, kuma a gudanar da irin wannan aiki a makaranta. Mataki na farko shi ne, kiyaye yaren kabilar Du Long, mista Yang ya bayyana cewa, 

"Mun samu wani babban ci gaba, wanda ya keta shekaru sama da dubu daya, hakan ya sa mai yiwuwa yaranmu, za su manta da tarihinmu. Don haka, mun kafa kwasa-kwasai da harsuna biyu, wato harshen Han da na Du Long, don koyar da su kan yaya za a rubuta da karanta yaren Du Long."
Malam Ma Jianxin ya soma aikin koyarwa da harsuna biyu a makarantar tun daga shekarar 2006, wanda kuma ya kasance malami daya tilo dake ba da ilmi da harsuna biyu. A farko, ana koyarwa da harsuna biyu ne domin samar da sauki ga dalibai masu iya magana da harshen Du Long kawai, wajen koyon harshen Han. Nan da shekaru sama da 10 da suka gabata, burin koyarwa ya canja zuwa taimakawa dalibai wajen tunanin harshen kabilarsu. Malam Ma ya ce, 

"Harshen Du Long harshe ne na karamar kabila, sakamakon tasirin da al'adun waje ke kawowa Abu ne mai wahala dalibai su iya mafani da harshen kabilarmu don yin mu'ammala. A gani na, kiyaye harshen kabilarmu na da muhimmanci sosai. Ina damuwa watakila harshenmu zai bace sannu a hankali. Ya kamata mu mai da hankali kan yada al'adunmu. A da, yara suna iya rera wakokin na kabilar Du Long, amma yanzu mutane ciki har da mu malamai ba ma iyawa, dalilin shi ne, babu wata hanyar da ta dace wajen koyon al'adun kabilar ta mu."

Kabilar Du Long: Inganta nasarorin da aka cimma a fannin kawar da talauci ta hanyar yada al'adun kabila


A cewar malam Ma Jianxin, a nan gaba zai tattara wasu wakokin na kabilar Du Long, domin koyarwa dalibai a kwasa-kwasai, kamar yadda 'yan kabilar suke yi a da, wato su rera, da tunanin tarihi da labarai game da kabilarsu ta hanyar rera wakoki daga zuriya zuwa zuriya.

Ban da wannan kuma, a lokacin hutu tsakanin kwasa-kwasai, dalibai su kan yi raye-raye tare. Kabilar Du Long wata kabilar ce mai kwarewa kan rera wakoki, da yin raye-raye, a duk lokacin bukukuwa, ko yayin da ake aiki, sukan rera wakoki da yin raye-raye.
Ma Guoxian, mai aikin sa kai ne da ya fito daga jami'ar Yunnan ta kasar Sin, a yayin da yake neman digiri na biyu, ya zo makarantar dake garin Du Long Jiang don koyarwa. A farkon lokacin da ya iso nan a watan Satumba na shekarar 2018, sai al'adun gargajiyar kabilar Du Long ya jawo hankalinsa sosai. Ma Guoxian dake koyon fasahar tsare-tsare kan tufafin kabilu, ya bullo da wani tunani, wato yana fatan hada kan fasahar musamman ta Batik, da ta Bandhnu ta lardin Yunnan, da salon musamman na kabilar Du Long, ta yadda dalibai za su iya bayyana al'adun kabilar Du Long ta hanyar amfani da fasahar Batik, da ta Bandhnu. Ma Guoxian ya ce, 

"Ina fatan koyar da yara fasahar Batik da ta Bandhnu dake iya wakiltar al'adun lardin Yuannan, sabo da duk fasahohin biyu abubuwan tarihi ne na al'adu da ake gada daga kakannin kakanni na kasar Sin. Ta hakan yaran za su iya bayyana abubuwan dake cikin al'adun kabilarsu ta Du Long, ta hanyar amfani da fasahohin biyu."

A watan Oktoba na shekarar 2018, Ma Guoxian ya gabatar da shiri game da haka ga shugaban makarantar ta Du Long Jiang da jami'arsa ta Yunnan, wanda ya samu goyon baya sosai daga bangarorin biyu, har ma sun samar da isassun kudi cikin lokaci domin tabbatar da shirin.

Bayan an kafa kwas na koyar da fasahohin, daliban da suka yi rajistar domin shiga kwas din sun yi yawa, kuma karfin kirkira da basira da suka bayyana sun baiwa Ma Guoxian mamaki sosai. A cewarsa, watakila wannan ya dogaro ne kan karfin kabilarsu, na bayyana abubuwa masu kyau.