Wang Jianguo: Ya canja rayuwarsa ta hanyar wasannin motsa jiki
2020-01-13 13:15:49 CRI
Da karfe 5 na sassafiyar kowace rana, kungiyar wasan tafiya da kafa cikin sauri ta Wanbuyouyue dake birnin Cangzhou a lardin Hebei na kasar Sin ke fara yin wasan motsa jiki. Dukkan membobin kungiyar suna zuwa wurin yawon shakatawa na Renmin na birnin a wannan lokaci, don yin tafiya da kafa cikin sauri.
A kan ga wani mutum da yake yin tafiyar a farkon jerin gwanon 'yan kungiyar, wanda ke kan kujerar guragu. Sunansa Wang Jianguo. Wang Jianguo yana da kirki, dana kyautatawa sauran mutane, da kuma sa kaimi gare su wajen kara samun ci gaba a rayuwarsu, don haka mutanen dake kewayensa su kan kira shi da sunan "Dan uwa na biyu".
Wang Jianguo yana da shekaru 62 da haihuwa, yana kuma da son wasannin motsa jiki, kuma ya taba samun kwarewa a wasan dambe, da wasan kokawa, da iyo, da wasan kwallon kwando. Amma wani hadarin jirgin kasa da ya faru ba zato ba tsamani ya canja rayuwarsa. A wata rana cikin shekarar 1983, Wang Jianguo wanda ke gudanar da aikin shirya jiragen kasa a tashar jiragen kasa ta birnin Cangzhou ya rasa kafafu biyu, a sakamakon hadarin jirgin kasa don ceton matashi mai koyon fasahohinsa. Hadarin ya kawo babbar illa ga rayuwarsa da halin zuciyarsa, yana jin rashin ma'ana a rayuwarsa, ya kan ji rashin jin dadi har ma da yawan fushi. Matarsa Wang Yufeng tana kulawa da shi sosai, ta kan yin hira da shi, da sa kaimi gare shi don samun farfadowa. Madam Wang Yufeng ta bayyana cewa, "Lokacin da ya ji rashin dadi, sai na gaya masa cewa, mu fuskanci halin da ake ciki a yanzu tare. Duk irin mawuyacin halin da yake fuskanta, zan zama tare da shi, ba zan bar shi ba. Ban taba yin husuma da shi ba, na taimaka masa wajen kyautata halin zuciyarsa sannu a hankali." A sakamakon kyakkyawar kulawa da matarsa ke bashi, Wang Jianguo ya samu farfadowa sannu a hankali. A watan Agusta na shekarar 1987, Wang Jianguo yana kallon telebijin, ya ga gasar wasanni ta nakasassu ta kasar Sin karo na biyu, inda 'yan wasa nakasassu suka yi kokari, da yin gasa don neman samun lambobin yabo a wasanni, wadanda suka burge Wang Jianguo sosai. Ya ji yana son halartar gasar wasanni ta nakasassu, don canja rayuwarsa ta wasanni. Bisa goyon bayan da iyalai da abokansa suka nuna masa, Wang Jianguo ya zabi yin horaswa kan wasan jefa kwallon karfe, da wasan iyo, da kuma tseren kujerar guragu, kuma ya yi kokarin samun horo a kowace rana. A shekarar 1990, ya halarci gasar wasanni ta nakasassu ta birnin Cangzhou, inda ya karya matsayin bajintar wasan iyo na kasar Sin. A sakamakon hakan, hukumar da abin ya shafa ta birnin Cangzhou, ta bada shawara da a sa shi ya halarci gasar wasanni ta nakasassu ta lardin Hebei a shekarar 1991, inda ya sake karya matsayin bajintar wasanni na kasar Sin guda biyu. Daga baya, hukumar da abin ya shafa ta lardin Hebei ta gabatar da shi don halartar gasar wasanni ta nakasassu ta kasar Sin ta shekarar 1992, inda ya samu lambobin yabo na zinari guda biyu, da kuma lambar yabo ta azurfa daya. A ganin Wang Jianguo, ba ma kawai wasannin motsa jiki sun canja rayuwarsa ba ne, har ma sun kara bude idanunsa, da sa kaimi gare shi wajen kara samun ci gaba. Wang Jianguo ya bayyana cewa, "Wasannin motsa jiki sun canja rayuwata sosai, bayan da na yi horaswa da halartar gasar wasanni, an kara bude min idanu na, tunanin wasanni ya sa kaimi gare ni wajen kara samun ci gaba. Idan ban motsa jiki a wata rana ba, sai in ji kamar ban gama wani aiki ba." Wang Jianguo ya halarci gasannin wasanni na nakasassu har na tsawon shekaru 20, inda ya samu lambobin yabo manya da kanana da dama. Bayan da ya yi ritaya daga wasan, ya ci gaba da motsa jiki a kowace rana. A birnin Cangzhou, wasan tafiya ta kafa cikin sauri ya fi samun karbuwa, akwai kungiyoyi fiye da 20 na wannan wasa a birnin. A shekarar 2016, an kafa kungiyar wasan motsa jiki da wasan tafiya da kafa cikin sauri ta birnin Cangzhou, sai Wang Jianguo ya shiga kungiyar nan da nan, da halartar ayyukan wasan da kungiyar ke shiryawa.