logo

HAUSA

Ilmin gishirin rayuwa<?xml:namespace prefix = o ns = "urn:schemas-microsoft-com:office:office" />

2020-01-11 19:21:00 CRI



A yayin da hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ke dada bunkasa a fannoni daban daban, al'ummar sassan biyu ma na kara cudanya da juna, hakan nan kuma suna ta kara sha'awar al'adun juna da kuma kara nazarin harsunan juna. A nan kasar Sin, an kafa sassan koyar da harsunan kasashen Afirka a jami'o'i da dama, kuma Hausa na daga cikin harsunan da ake koyarwa. Professor Salisu Ahmed Yakasai shi yake koyar da harshen a jami'ar koyon harsunan waje ta nan birnin Beijing, kwanakin baya ne, wakiliyarmu Lubabatu ta tattauna tare da shi. Ku biyo mu cikin shirin, don jin yadda Professor Salisu Ahmed Yakasai yake gudanar da harkokinsa na malanta a kasar Sin cikin tattaunawarsu da Lubabatu.