Shin ya kamata a yi tattalin kudi sabo da wata rana?
2020-01-09 16:12:06 CRI
A cikin wannan sabon shiri na Duniyarmu A Yau, baki wadanda suka halarci tattaunawa sun yi musayar ra'ayoyinsu kan batun "Shin ya kamata a yi tattalin kudi zuwa wani lokaci ko kuwa a yi amfani da su lokacin da suka samu?"
Malam Yahaya Babs ya ce, ya dace a yi tattali sabo da gobe. Kudin da ake da ajiye a yi tanadi a yi tattalin shi, kar a kashe su a lokacin da suka shigo. A ganinsa, ita rayuwa gaba daya, ana son a yi tattali, a yi tanadi. Haka, yau da gobe sai Allah, wannan gaibiyya ne. Yadda ka san kana yaro, aka haife ka, ka girma, kullum kana tunanin ka ga gobe. Kana girma, kana da buri. Idan ka yi girma, za ka yi aure. Idan ka yi aure, kana tunanin z aka yi haihuwa. To, shi kudi yana cikin yanayin rayuwa ma gaba daya. Sabo da za ka biya bukata, za ka ci ka sha.
Amma malama Hauwa Ibrahim Bello ta ce, yayin da kudin ke shigowa, a dace a kashe su, ba bukatar a yi tattali, a ajiye su. Dalilin da ya sa malama Hauwa ta yi tunanin haka shi ne, kana uziri da buri wanda ya dace a ce ka yi amma ba ka yi su ba kana jiran gobe, kuma goben nan ba nawa ba ne. Bugu da kari, idan a yi tattalin kudi, za ka bar kudin ka bar danka, sai danka ya zo ya yi almubzzaranci da kudin da ka dage ka nema. Sabo da haka, ya kamata a yi abun da ya dace da kudi lokacin da yakamata.