ShinYin kudi dare daya yana da kyau?
2020-01-02 10:30:59 CRI
A cikin wannan sabon shiri na Duniyarmu A Yau, baki wadanda suka halarci tattaunawa sun yi musayar ra'ayoyinsu kan batun "ShinYin kudi dare daya yanada kyau?". Malam Yahaya Babs ya nuna goyon baya ga lamarin yin kudi dare daya. A ganinsa, idan ya samu arziki dare daya, wannan alheri ne Allah ya kawo masa. Amma Malam Ni'ima ba ta yarda da ra'ayinsa ba, inda ta ce, idan wani ya samu arziki dare daya ba tare da yin kokari ba, wannan arziki zai illata halinsa. Ya kamata a samu arziki bisa kokarin da ya bayar. Ga tattaunawar da suka yi. (Ibrahim, Fatimah Jibril, Yahaya, Ni'ima)