logo

HAUSA

Kasar Sin ta baiwa makarantar dake babbar unguwar matalauta ta biyu a kasar Kenya kyaututtukan sabuwar shekara

2019-12-17 07:44:45 CRI

A yayin da ake shirin shiga sabuwar shekarar 2020, a ranar 11 ga watan Disamban shekarar 2019 dake shirin karewa, jakadancin kasar Sin dake kasar Kenya ya baiwa makarantar Mcedo Beijing dake unguwar matalauta ta Matsare tallafin kayayyaki, ciki har da abincin safe da na rana, kayayyakin wasanni, abinci da wasu kyaututtukan sabuwar shekara, wadanda suka samu karbuwa sosai daga wajen yara. To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau za mu kawo muku bayani ne gama da haka. A wannan wata da muke ciki, kasar Kenya ta gamu da ambaliyar ruwa da ba a taba ganin irinsa ba a cikin 'yan shekarun da suka gabata, sakamakon haka, hanyar dake unguwar matalauta ta Matsare dake gabashin Nairobi, babban birnin kasar ta cika da tabo. Unguwar matalauta ta Matsare, ita ce unguwar matalauta ta biyu a kasar Kenya, makarantar Mcedo Beijing tana dab da wata babbar hanya dake unguwar. Ofishin jakadancin kasar Sin dake Kenya ne ya samar da kudi don kafa wannan makarantar a shekarar 2007, kuma a shekarar 2012 aka habaka ta. Yanzu haka, akwai dalibai sama da 500 da suka fito daga unguwar matalauta ta Matsare dake karatu a makarantar. Selvin Kasowa 'yar shekaru 15 tana daya daga cikinsu. "A Matsare na girma, kane na da kanwa ta ma a nan suke karatu. Don haka, dole mu yi kokari domin mu inganta rayuwarmu, da ma cimma burinmu." Selvin Kasowa, tana da burin zama yar wasan kallon kafa. Yanzu haka, tana wasa a kulob din kwallon kafa na makarantar Mcedo Beijing. A yayin bikin ba da tallafi da aka shirya a ranar 11 ga wata, majalisar tattalin arziki da cinikayya ta kasashen Kenya da Sin ta samar da kayayyakin wasannin kwallon kafa da darajarsu ta kai dala kusan 3000 ga wannan kulob, hakan ya faranta ran Selvin Kasowa sosai, saboda ta samu sabbin takalma da rigunan wasan kwallon kafa "Wasan kwallon kafa ya kan taimakea min wajen mantawa da abubuwan da suka dame ni, ina godewa masu horas da mu domin goyon bayan da suke ba mu na koyon dabarun wasan kwallon kafa. A yau kuma, an ba mu wadannan kayayyakin wasan kwallon kafa, gaskiya mun yi godiya kwarai da gaske." Sunan kulob din kwallon kafa da Selvin Kasowa ke ciki shi ne "Beijing Ranger", ya samu wannan suna ne sakamakon tallafin da kasar Sin ta baiwa kulob din. Yan wasan kulob din sun taba shiga gasar wasan kwallon kafa na kasar Kenya. Shugaban makarantar Mcedo Beijing, Benedict Kiage ya gayawa wakilinmu cewa, ga wadannan yara mata dake wurin, wasan kwallon kafa na almanta neman cimma buri da sauyin rayuwa. "Muna da kungiyar wasan kwallon kafar mata, inda muke koyar da yara mata wasan kwallon kafa. Wasan zai taimak musu wajen shiga makaranta. Don haka, mun yi godiya sosai ga kasar Sin saboda kwallon kafa da sauran kayayyakin da ta samar wa wadannan yara mata." Benedict Kiage ya girma ne a unguwar matalauta ta Matsare, bayan ya kammala karatunsa sai ya dawo nan, don ya zama malami a nan. A ganinsa, samun ilmi na iya canja makomar mutum, haka lamarin yake ga yaran dake unguwar matalauta. Ya ce, yara suna shawarar fahimtar abubuwan dake faruwa a sassan duniya, "Abun da ya zama dole na fada shi ne, a yayin da muke shirin shiga sabuwar shekara, yaran dake unguwar matalauta suna son su yi murnar bikin tare da mutanen da suka kawo ziyara a nan. Don haka, ofishin jakadan kasar Sin da majalisar tattalin arziki da cinikayya ta Kenya da Sin sun ba mu tallafi a wannan lokaci, hakan wani abu ne mai faranta rai sosai." Mashawarci a fannin kasuwanci a ofishin jakadancin kasar Sin dake Kenya mista Guo Ce ya bayyana cewa, a gabannin sabuwar shekara, ofishin jakadancin Sin ya tsaida kudurin rika samar da abinci na safe da na rana a ko wace rana na tsawon shekara guda. Majalisar tattalin arziki da cinikayya ta Kenya da Sin ma ta ba da tallafin abinci da wasu kyaututtuka da kuma na'urorin daukar hotunan bidiyo ga wadannan yara. Ya bayyana cewa, yana fatan ganin, kamfanonin kasar Sin dake Kenya za su kara daukar nauyin dake bisa wuyansu na taimakawa al'ummar kasar. "Na yi imanin cewa, kyautar abincin safe da na rana za su taimakawa wadannan yara ta yadda za su girma yadda ya kamata. A waje guda kuma, majalisar kamfanonin kasar Sin dake Kenya ita ma ta shirya ayyukan ba da tallafi, inda kamfanin Startime da China Telecom da sauransu dukkansu sun ba da taimako. A nan gaba kuma, za mu karfafawa kamfanonin kasar Sin dake Kenya gwiwa don su kara daukar nauyin taimakawa al'ummar kasar, kamar mayar da hankali kan zaman rayuwar yaran dake zama a unguwoyin matalauta, wannan muhimmin sashe ne da za mu dora muhimmanci kansu." A karshe, Selvin Kasowa ta gayawa wakilinmu cewa, ko da yake a cikin sunan makarantarsu akwai Kalmar "Beijing", amma ba ta taba kai ziyara a kasar Sin ba, tana fatan wata rana, za ta ziyarci Beijing.

"Ina fata wata rana zan kai ziyara birnin Beijing, har ma na yi abokai da dama a birnin. A gani na, suna da kirkir kwarai."(Bilkisu)