Xu Aiju: Yin amfani da fasahar saka wajen cimma burinta na taimakawa wasu mata
2019-12-13 20:25:25 CRI
A birnin Cangzhou da ke lardin Hebei na kasar Sin, akwai wata mace mai rike da fasahar saka sosai. A cikin shekaru fiye da 20 da suka gabata, tana martaba ka'idar "yin amfani da fasahar saka wajen cimma bur,i da ma taimaka wa saura domin ana iya ganin hasken rana a ko ina", kuma ta raya aikinta bisa fasahar saka ta gargajiyar Sin wajen samun abin dogaro da kai, lamarin da ya sa ta taimakawa mata masara aikin yi, da manoma mata fiye da 3000 wajen cimma burinsu na kau da talauci da samun wadata. Wannan macen ita ce Xu Aiju, babbar manajar kamfanin samar da kayayyakin saka na Dongjucaili.
A shekarar 1997, Xu Aiju mai shekaru 28 da haihuwa, aka sallame ta daga aiki, sakamakon sauyawa tsarin kamfanin da take ciki, lamarin da ya sa ta rasa abin dogaro da kai. Domin ci gaba da rayuwa, Xu ta fara zuwa birnin Beijing don sayar da zanen tebur. Yayin da take tuna da yadda take kokarin yin kasuwanci a wancan lokaci, ta bayyana cewa, wahalhalu iri daban daban da ta sha, kamar zama a dakin da ke karkashin kasa, da shan jin maganganun ba'a da aka sha yi mata da dai sauransu, duk wadannan sun ba ta damar karfafa zuciyar ta wajen daina yin watsi da wani abu. Xu tana mai cewa,
"Idan akwai hanyoyi 100 a gabanka, kada ka gwada 99 kawai, watakila za ka ci nasara idan ka zabi hanya ta 101. Wannan ra'ayi ya taimaka min sosai yayin da nake raya aiki, wato ya kamata a yi iyakacin kokari wajen yin ko wane aiki, kada a fid da tsammanin yin kokari cikin sauki." A saboda martabar wannan ra'ayin, Xu Aiju ta fara kama wata hanyar da ta fi kyau wajen samun nasara. Yayin da Xu Aiju ke shiga wani kwas din horaswa da birnin Cangzhou ya shirya don mata marasa guraban aikin yi, ta gano cewa, akwai dimbin 'yan uwanta mata da ke fuskantar matsalar da ta taba addabarta, wato ba su san inda za su nufa ba a nan gaba, ba su iya gano makomarsu ba. Sakamakon gogewarta ta raya aiki, Xu ta fahimci matukar wahalhalun da marasa guraban aikin yi musamman ma mata ke fuskanta. Don haka, la'akari da kwarewar mata wajen fasahar saka, da ma kulawar gida da ake bukatarsu su yi, Xu ta tsai da kudurin kafa wani kamfanin samar da kayayyakin saka, domin daukar wadannan matan, ta yadda za su iya samun abin dogaro da kai.
Ga mata, aikin saka ba abu ne mai wuya ba, amma yadda kayayyakin saka za su iya samun karbuwa a kasuwa, ba abu ne shi ma mai sauki ba ne. Don haka, bayan kafuwar kamfanin, binciken kasuwa, neman samun damar kasuwanci, wani muhimmin aiki ne ga Xu Aiju. Ta fara yin tafiya a manyan biranen Sin, kamar su Beijing, Shanghai, Guanzhou domin neman samun oda. Domin rage yawan kudin da ake kashewa, kullum ita kadai take yin tafiyar, ta sayi tikitin jirgin kasa mafi araha, ta zauna a otal mafi rahusa, ta je kasuwanni daya bayan daya da kafafunta, a karshe dai, ta samu oda da dama. A ganin Xu Aiju, yanzu ko aikin zai samu nasara ko a'a ba abun da ya shafe ta ita kadai ba ne, abu ne da ke da nasaba da 'yan uwanta mata daruruwa. Xu ya furta cewa,
"Yayin da nake kokarin raya aiki a Beijing, ni kadai ce, don haka na fi samun yawan sassauci. Amma yanzu yayin nake shirin tafiya don neman kasuwa, ta idanun ma'aikata 'yan uwana mata, ina iya ganin yadda suke sa rai ga odar da zan iya kawo musu. Don haka akwai nauyi a wuyana, ba na iya yin kasa a gwiwa ga wahala. Ko da akwai matukar gajiya, bayan dan huta kadan, ina ci gaba da tafiyata."
Tun bayan da ta kafa kamfanin, Xu Aiju na tsayawa tsayin daka kan daukar ma'aikata daga cikin mata marasa guraban aikin yi, da ma manoma mata. Sannu a hankali, ta kafa cibiyoyin samar da kayayyakin saka na unguwanni da gundumomi na birnin Cangzhou, har ma da wasu wurare daga lardin Shandong, wadanda yawansu ya kai 16, lamarin da ya sa mata fiye da 3000 suka samu damar samun abin dogaro da kai, ciki har da mata masu bukatar musamman kimanin 200.
Wang Jinying mai shekaru 65 da haihuwa, wata manomiya ce a kauyen Shanhou da ke gundumar Haixing ta birnin Cangzhou. Ko da yaushe tana sha'awar fasahar hannu, kuma ta taba saka huluna da tufafi a lokacin da ba take shan ayyukan gona, domin sayar da su a kasuwa don kara kudin shiga. Wang ta bayyana cewa, a wancan lokacin, yawan kudin shigar ya kai Yuan 200 a ko wane wata. Amma bayan da ta fara samun aikin saka daga wajen kamfanin Xu a shekarar 2009, yawan kudin ya karu sosai, har ma ya zarce Yuan 2000 a ko wane wata, sakamakon karuwar yawan kayayyakin da ake bukatar sarrafawa, da ma karuwar farashin kayan. Yanzu Wang shugaba ce ta wata cibiyar samar da kayayyakin saka, kuma akwai mata masu fama da talauci fiye da 130 dake aiki tare da ita. Wang ta ce, "A wancan lokacin da nake yankin karkara, ina fama da talauci sosai, Manaja Xu ta taimaka min. Yanzu na ga akwai wasu wadanda ke fama da talauci a kewayena, don haka na taimaka musu. Tun bayan da suka fara aikin samar da kayayyakin saka, zaman rayuwarsu ya kyautata, ganin haka, na ji dadi sosai, lamarin da ya kara karfafa zuciyata wajen ci gaba da aikin."
Domin kyautata kwarewar mata masu aikin saka, da kuma samar da kayayyakin da ke iya biyan bukatun kasuwa, Xu Aiju na mai da hankali kan aikin horaswa. A ganinta, kayan fasahar hannu sun sha bamban da saura, ana bukatar a yi amfani da fasahar wajen bayyana abun da ake ji a rai. Don haka, ban da koyar da fasahohin saka, kullum ta kan gayyaci kwararrun da abubuwa masu nasaba da hakan, da kwas din horaswa kan sabbin nau'ikan kayan fasahar hannu na zamani, da ma ilmin amfani da launuka daidai a tufafi, ta yadda za su dace da juna, sa'an nan ta kara kwarin gwiwar matan wajen fita daga gida don bude idanunsu, ta yadda za su iya samar da kayayyakin saka mafi ingani da kyan gani. Kyautata kwarewar mata wajen aiki ba domin su samar da kayayyaki ga kamfaninta kawai ba ne, Xu Aiju ta ce, yadda za a sa kaimi ga karin matan wajen raya ayyuka da kansu, hanya ce da take bi a ko da yaushe. Tana mai cewa,
"Idan kin koyi fasahar saka kawai, to za ki zama kamar wata na'urar sarrafarawa. Idan babu buri, to babu makoma. Don haka yayin da nake horar da su, na kan karfafa zukatan ma'aikatanmu mata wajen raya ayyukansu gwargwadon karfinsu."
Gong Ercui mai shekaru 28 da haihuwa, tana daya daga cikin wadanda ke kokarin amfani da hannayenta don kago makomarta mai haske. Tun Gong Ercui tana karama, tana da nakasa a kafa. Ko da yaushe tana kokarin samun abin dogoro da kai, amma ta gaza samu. Aikin samar da kayayyakin saka da ta samu a wajen Xu Aiju ya bude mata wata kofar cimma burinta. Amma a matsayinta ta wata matashiya, ba ta gamsu da yin aikin sassafawa kaya da hannu kawai ba, tana da wani babban buri na daban, wato tana son ta nemi sayar da kayayyakin da kanta, wanda ya samu goyon baya sosai daga wajen Xu Aiju. Sakamakon samun nakasa a kafa, ta samu wata hanya ta daban wajen sayarwa, wato ta fara sayar da kayayyakin saka ta dandalin daukar bidiyon kai tsaye da ke shafin Intanet. Kwalliya ta biya kudin sabulu, kayayyakinta sun samu karbuwa a Intanet, har ma yawan kudin da take samu ya kai Yuan 1000 a ko wane wata. Gong Ercui ta ce, ta yi wa Madan Xu godiya sosai, in ba don ita, da ba za ta iya shiga yanayi mai matukar kyau kamar na yanzu ba. Ta kara da cewa,
"Mutane masu bukatar musamman kamar ni, na da matukar wuya mu iya samun aikin yi, don haka idan ina iya samun abun dogoro da kai, ina jin gamsuwa kwarai da gaske. Yanzu ina da kudin shiga, ina iya ciyar da kaina bisa kudin da ni kaina na samu. Da ganin wadannan kayyayakin saka da na yi, na yi farin ciki sosai. Zaman rayuwata cike yake da hasken rana."
Bayan da kamfanin ya samu bunkasuwa cikin shekaru 15 da suka gabata, yanzu nau'ikan kayayyakin saka da kamfanin Xu Aiju ya samar ya zarce dubu daya, wadanda suka shafi fannonin kayan gida, hula, 'yar tsana, da ma kayan kirkire-kirkire na hannu. Haka kuma bisa ikon mallakar ilmin kirkira guda tara da kamfanin ya samu, yanzu tambarin kamfanin mai suna "Aiyangyang" ya riga ya samu karbuwa sosai a duk fadin kasar Sin. Irin nasarar da ta samu ba ya dakatar da taken Xu Aiju na ci gaba. Tana hadin gwiwa tare da nagartattun kungiyoyin tsara fasali na kwalejin zane-zane ta Jami'ar Tsinghua, da na kwalejin koyar da ilmin tufafi ta Beijing, a kokarin raya kasuwannin gida da na ketare a waje daya.
A yayin bikin baje kolin kayayyakin da ake shigar da su kasar Sin karo na biyu da aka yi a 'yan kwanakin baya a birnin Shanghai, Xu Aiju ta nuna kayayyakinta ga 'yan kasuwa daga kasar Bangladesh da kasar Sri Lanka, wadanda suka amince da su sosai, har ma sun daddale yarjejeniyar hadin gwiwa, lamarin da ya sa kayayyakin saka na gargajiyar kasar Sin suka samu damar fita zuwa ketare. Xu Aiju ta ce,
"fasahar hannu ta gargajiyar kasar Sin ta kasance kamar wani lu'u lu'u mai daraja sosai, amma dimbin kasashe ba su san ta sosai ba. Ta shiga bikin, za mu iya yada fasahar hannu ta kasar Sin da sauran kasashe. A waje daya kuma, za mu shigo da wasu fasahohin hannu nasu, domin a hada fasahohinmu na gida da na waje tare, yayin da muke samar da kayayyakin saka a nan gaba, ta yadda dukkan al'ummmun duniya za su more makoma mai kyau baki daya."
Xu Aiju, tana daya daga cikin wadanda suka ba da taimako ga mata wajen fitar da su daga kangin talauci a birnin Cangzhou. Bisa labarin da muka samu, an ce, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, birnin ya sa kaimi sosai ga amfani da fasahar hannu wajen fitar da mata daga fatara da ma samun wadata. Domin cimma wannan buri, birnin ya kafa kungiyar samar da kayayyakin hannu, da ma tasoshi 19 na ba da hidimar rayar sana'o'in hannu, da cibiyoyin sarrafa kayayyakin hannu 150, wadanda suka shafi fasahar saka, da fasahar dinki, da fasahar yanka takarda da ake yi da almakashi, da fasahar yin amfani da allura da zare domin yin ado kan kyalle ta hanyar dinki, da dai sauransu. Matakin da ya bai wa mata kimanin dubu 100 damar samun wadata, wadanda matsakaicin yawan kudin shigar su ya kai daga Yuan dubu 5 zuwa dubu 50 a ko wace shekara.(Kande Gao)