logo

HAUSA

Wasu daga cikin abubuwan da suka faru a Afirka a shekara ta 2019

2019-12-12 08:52:53 CRI

Masu iya magana na cewa, "shekara kwana" a ranar Litinin 31 ga watan Disamba na shekara ta 2019 miladiya ta kawo karshe, kuma kamar sauran shekaru da suka gabaci wannan shekara, abubuwa da dama sun faru, kama daga na ban-al'ajabi, mamaki, tausayi, bajinta, takaici, tashin hankali da dai sauransu.

Wasu daga cikin abubuwan da suka faru a Afirka a shekara ta 2019

Misali a watan Janairun shekara ta 2019 ne, wasu sojoji suka yi yunkurin juyin mulki a kasar Gabon, kana a watan Fabrairu, tsohon shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir, ya ayyana dokar ta baci a kasar, wanda daga bisa ni sojoji suka hambarar da shi daga karagar mulki.

Wasu daga cikin abubuwan da suka faru a shekarar 2019 mai shirin karewa a nahiyar Afirka, sun hada da saukar shugaban Aljeriya Abdelaziz Bouteflika daga mulki, bayan boren da 'yan kasar suka gudanar na neman ya sauka daga mulki.

Wasu daga cikin abubuwan da suka faru a Afirka a shekara ta 2019

Bugu da kari a shekarar dake karewar ce, aka kaddamar da taron zuba jari na Afirka a kasar Masar, a shekarar ce kuma mutane 37 suka mutu, sanadiyar zabtarewar kasa a yankin Pokot na kasar Kenya.

A watan Nuwanban shekarar 2019 ne, gidauniyar Jack Ma na kasar Sin, ta karrama mutane 10 da suka yi fice a fannin tsaron gandun daji a Afirka. A shekarar ce kuma, aka shirya taron yawan al'umma na kasa da kasa a Kenya. Haka nan, a watan Oktoban shekarar 2019 mai shirin karewa, kamfanin StarTimes na kasar Sin, ya kammala aikin samar da talabijin na zamani a kauyuka 1,000 a Najeriya.

Wasu daga cikin abubuwan da suka faru a Afirka a shekara ta 2019

A shekara ta 2019 ne kuma, shugaban kasar Angola ya kaddamar da filin jirgin sama da kasar Sin ta gina a kasarsa

Muna fatan samun zaman lafiya, kwanciyar hankali, alheri da karuwar arziki a duniya baki daya a sabuwar shekarar 2020, Amin. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)