Muhimmancin hadin gwiwar kasar Sin da Afrika
2019-12-05 08:46:05 CRI
Kimanin sama da shekaru 5 ke nan, tun bayan da shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya yi bayani game da manufar kasar Sin ga nahiyar Afrika a Tanzania, wadda ta tsara makomar huldar kasar Sin da Afrika a sabon zamani, wadda yanzu haka ta haifar da kawance da kulla dangantaka da yarda da juna tsakanin bangarorin biyu.
Ita dai wannan manufa da shugaba Xi ya gabatar, yayin ziyarar farko da ya kai nahiyar Afrika, a matsayinsa na shugaban kasar Sin, a shekarar 2013 ta dogaro ne bisa gaskiya da samun managartan sakamako da fahimtar juna,
Bisa wadannan tsare-tsare, Kasar Sin da Afrika, sun hada karfi da karfe, wajen samar da tafarkin samun ci gaba na bai daya, wanda ke da nufin samar da dangantaka mai karfi da ba a taba samun irinta ba, tsakanin kasar ta nahiyar Asia da kuma nahiyar Afrika, wadanda yawan al'ummarsu ya kai biliyan 2.5, kwatankwacin daya bisa ukun al'ummar duniya baki daya. Bayan wadannan shekaru, ana iya ganin dimbin moriyar da aka samu bisa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da nahiyar Afrika a fannoni da suka hada da tattalin arziki, Ilimi, cinikayya, kayayyakin more rayuwa, al'adu, noma, raya masana'antu da ma kaiwa juna ziyara a bangare manyan jami'ai da ma shugabanni.
Tarukan dandalin hadin gwiwar kasar Sin da nahiyar Afrika FOCAC, da suka gudana a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu,da Beijing na kasar Sin gagarumin ci gaba ne ga dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu. Wadanda ke aikewa da muhimmin sako ga al'ummomin duniya cewa, Sin da Afrika sun hada hannu don samun nasara tare.
Ana sa ran, kasashen Afrika da Sin za su hade manufofin da dabarunsu na samun ci gaba karkashin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" da muradun ci gaba masu dorewa na MDD da kuma ajandar Tarayyar Afrika da ake son cimmawa zuwa 2063. Alakar sassan biyu, tana kara taka muhimmiyar rawa a fannonin rayuwar bil-Adam, matakin da masana suka yaba matuka. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)