MDD ta shirya gagarumin biki don murnar ranar yara ta duniya
2019-11-28 09:31:34 CRI
A shekarar 1954, babban taron MDD ya zartas da wani kuduri na kafa ranar yara ta duniya a dukkan kasashen duniya. Daga baya kuma a ranar 20 ga watan Nuwamba na shekarar 1989, babban taron majalisar ya zartas da jarjejeniyar kare hakkokin yara. Sa'an nan daga shekarar 1990, MDD ta fara shirya biki a ranar 20 ga watan Nuwamba, don murnar ranar yara ta duniya, da ma tunawa da kulla yarjejeniyar.
A bana kuma,aka shirya gagarumin biki a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York a kwanan baya, don murnar ranar yara ta duniya ta shekarar 2019, tare kuma da tunawa, da cika shekaru 30 da kulla yarjejeniyar kare hakkokin yara.(Kande Gao)