Hira da Alhaji Lawal Alhassan darakta janar na hukumar janyo masu zuba jari ta jihar Kano a Najeriya (B)
2019-11-27 10:32:13 CRI
A makon da ya wuce, mun fara gabatar muku da wata hira da muka yi da Alhaji Lawal Alhassan darakta janar na hukumar janyo masu zuba jari a jihar Kano dake tarayyar Najeriya wato Kaninvest a takaice, hukuma ce da gwamnatin jihar Kano ta dorawa alhakin shiga sassa daban daban na ciki da wajen jihar har ma da kasashen ketare domin zawarcin masu zuba jarinsu a jihar. Jihar Kano tana shiyyar arewa maso yammacin Najeriya, ana mata kirari da "Kano ta dabo jalla babbar hausa Kano tunbin giwa ko da me ka zo an fi ka", jihar ta kasance babbar cibiyar kasuwanci ta arewacin Najeriya, ta shahara matuka a harkokin kasuwanci, akwai 'yan kasuwa daga sassa daban daban na ciki da wajen Najeriya da suke mu'amalar kasuwanci da jihar Kano. An shafe shekaru aru-aru ana mu'amalar kasuwanci tsakanin 'yan kasuwar jihar Kano da na kasar Sin, wannan ta sa ake kara samun hulda tsakanin al'ummomin bangarorin biyu, idan za'a iya tunawa ko da a kwanakin baya mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II ya nada wani basine mukamin sarkin Sinawan jihar Kano, al'amarin da ya kara haskakawa duniya irin girman alakar dake tsakanin jihar Kano da kasar Sin. Shi kansa gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya taba kawo ziyarar aiki a kasar Sin inda ya halarci wasu lardunan kasar domin kulla wasu muhimman yarjeniyoyi ciki har da batun yarjejeniyar bunkasa aikin gona a jihar da nufin bunkasa tattalin arziki jihar Kano. Gwamnatin Kanon ta kafa kwamitin bada shawarar nemo masu zuba jari a jihar wanda ta nada mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II a matsayin shugaban kwamitin, kuma kwamitin ya sha kai ziyarar aiki zuwa kasar Sin inda ya ziyarci wasu da dama daga cikin kamfanonin kasar, daga cikin kamafonin da tawagar suka nuna sha'awar janyo hankalinsu don zuba jarinsu a jihar ta Kano akwai kamfanonin saka tufafi, da kamfanin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana, da kamfanin samar da sukari ta hanyar masara da dai sauransu.
Idan za mu iya tunawa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kawo ziyarar aiki a kasar Sin har karo biyu domin kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma kulla yarjeniyoyi daban daban musamman kamfanonin samar da ayyukan kayayyakin more rayuwa, da suka hada da layin dogo, gine-ginen filayen jirgin sama da dai sauransu. Shugaban hukumar ta Kaninvest ya jaddada muhimmancin kyautata dangantaka tsakanin jihar Kano da kasar Sin har ma da Najeriya baki daya.(Murtala Zhang)