logo

HAUSA

Karfin tattalin arzikin Sin ya kara bayyana a ranar gwagaware ta bana

2019-11-21 08:45:38 CRI

Bayan kammala bikin baje koli na kayayyakin da aka shigo da su kasar Sin karo na biyu, sai kuma nan da nan aka shiga ranar gwagware ta ranar 11 ga watan Nuwamba a kasar Sin, yawan kayayyakin da aka sayar a bukukuwan biyu, sun nuna karfin kasuwar kasar na sayen kayayyaki. A yayin da tattalin arzikin kasar Sin ke fuskantar rashin tabbas a waje, kyakkyawar alama da kasuwar kasar ta nuna ta bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin na da makoma mai kyau a nan gaba, kuma yana cike da karfin tinkarar duk wani hadari da ka iya kunno kai

Karfin tattalin arzikin Sin ya kara bayyana a ranar gwagaware ta bana

Shagon sayar da kayayyaki ta Intanet na rukunin kamfanin Alibaba wato TMall, ya sayar da kayayyakin da darajarsu ta kai Yuan biliyan 10, kwatankwacin dala biliyan 1.43 a cikin minti daya da dakika 36,a ranar gwagaware ta kasar Sin da aka kaddamar da tsakar daren Litinin.

Da misalin sa'a daya da mintuna 26 da dakika 7 bayan tsakar daren, shagon na TMall ya sayar da kayayyakin da darajarsu ta kai Yuan biliyan 120.7, adadin da ya dara kayan da ya sayar a makamancin wannan rana a shekarar 2016. Dukkan wannan alkaluma, sun kafa wani sabon tarihi a ranar gwagawaren, wanda shagon na TMall ya tsara a ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 2009.

Karfin tattalin arzikin Sin ya kara bayyana a ranar gwagaware ta bana

A cewar kamfanin na Alibaba, sama da tanbarun kaya 22,000 na ketare daga kasashe da yankuna 200, sun shiga sayayyar wannan shekara a kasar Sin.

Wani mai bincike a cibiyar hadin gwiwar cinikayya da tattalin arzikin kasa da kasa dake karkashin ma'aikatar cinikiyya ta kasar Sin Zhou Mi, ya bayyana cewa, sabbin bayanan, sun nuna yadda tattalin arzikin kasar Sin ke kara karfi da fa'idar ci gaban fasahar zamani da cinikayyar kasa da kasa

Sayen kayayyaki na taka muhimmiyar rawa ga ci gaban tattalin arziki. Don haka, babbar kasuwar cikin gida ita ce ginshikin tattalin arzikin kasar Sin wajen fuskantar kalubale daga ketare da ci gaba da yin kwaskwarima da bude kofa ga ketare. (Ahmed, Saminu,Ibrahim/Sanusi Chen)