Ziyarar mataimakin gwamnan jihar Kano a kasar Sin
2019-11-13 13:54:40 CRI
A baya bayan nan ne wakiliyar sashin Hausa na CRI Fa'iza Muhammad Mustapha ta samu damar tattaunawa da Nasiru Yusuf Gawuna, mataimakin gwamnan Jihar Kano dake arewa maso yammacin Nijeriya, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin da kuma halartar taron kawancen birane a lardin Shandong na kasar, wanda kuma ke da nufin raya al'umma da kuma tattalin arzikin kasa. A cikin tattaunawar tasu, mataimakin gwamnan ya yi bayanin cewa kimanin shekaru 2 zuwa 3 da suka gabata, sun kulla hadin gwiwa da kamfanonin kasar Sin a fannonin aikin gona da masaka, wandanda dukkansu bangarori ne masu muhimmanci da za su haifar da ci gaba ga al'ummar jiharsa. Ya kara da yabawa ci gaban kasar Sin bisa yadda take sarrafa kayayyaki a cikin gida da kuma kyautata rayuwar al'umma.
Ga tattaunawar Fa'iza Mustapha da Nasiru Yusuf Gawuna mataimakin gwamnan jihar Kano, inda ya fara da yin cikakken bayani kan makasudin ziyararsa.(Murtala Zhang)