Labaran mata daga Tarayyar Najeriya
2019-11-11 16:45:47 CRI
A cikin shirinmu na yau, za mu gabatar mu da wasu labaran da suka shafi mata da muka samu daga Jaridar Leadership A Yau ta Tarayyar Najeriya.
Labari na farko shi ne game da yadda za a wayar da kan mutane musamman ma mata don rage cutar kansa
Uwargidan shugaban kasar Najeriya Aisha Buhari ta yi kira da a rika wayar da kan al'umma dangane da cutar daji, saboda a cewar ta hakan zai taimaka wajen hana yaduwar cutar a Nijeriya. Aisha ta bayyana hakan ne a taron wayar da kan mutane danagane da cutar wanda gidauniyar 'Medicaid Cancer' ta shirya. Ta ci gaba da bayanin cewar, kamata ya yi Nijeriya ta yi koyi da matakan kawar da wannan cuta da wasu kasashen Afirka suka dauka. Ta ce, "A yanzu haka wasu kasashen Afirka na yi wa mutane musamman ma mata allurar rigakafin cutar da ya kamata a ce mu bi wannan sahu a wannan kasar tamu Nijeriya." Bugu da kari kuma uwar gidan gwamnan jihar Kebbi kuma shugabar kungiyar 'Medicaid Cancer' Zainab Bagudu ta yi kira ga sauran sassan gwamnati da su hada hannu da gwamnati tarayya domin samar da kulawa ta gari wa masu fama da cutar kansa. Zainab ta ce kamata ya yi gwamnatocin jihohi da kuma kananan Hukumomi su taimaka wajen samar da na'urorin gwajin cutar da rage farashin magunguna domin tallafa wa rayuwar masu dauke da cutar a Nijeriya. Daga nan shugaban kungiya mai zaman kanta 'Monitor Health Care' Femi Ogunremi ya yi kira da gwamnati kan wayar da mata game da cutar dajin dake kama nono, mahaifar mace, cewar mata masu yawa na kamuwa da cututtukan a Nijeriya. Idan dai ba a manta ba a watan Fabrairu ne kungiya mai zaman kanta 'Project Pink Blue' ta yi wa mutane gwajin cutar daji kyauta a Abuja. Kungiyar ta yi haka ne domin wayar da kan mutane a kan ita cutar ganin cewar wadanda dauke da wannan cutar a Nijeriya na mutuwa saboda rashin samun kulawa wadda ta dace. Project Pink Blue ta yi kira ga mutane da su rika kulawa da irin abincin da suke ci tare da yawan motsa jiki, saboda akasarin haka na daga cikin hanyoyin kamuwa da cutar.
Masu sauraro, yanzu bari mu karkata mu leka zanga-zangar da kungiyoyi 20 na mata suka yi a Kano don batun satar yara.
Tawagar wakilan kungiyoyi 20 na mata zalla sun yi dandazo a majalisar dokokin jihar Kano domin gudanar da zanga-zangar neman mambobin majalisar su shiga maganar yaran nan guda 9 da aka gano a jihohin yankin kudu maso gabas bayan an sace su daga Kano. Kungiyoyin matan a karkashin hadakar kungiyar da malamai da sauran kungiyoyi masu zaman kansu (NGOs) sun bukaci majalisar ta kafa kwamitin bincike na musamman a kan lamarin. Shugabar wakilan kungiyoyin, Amira Shitu Abdulwahab, ta ce sun zo majalisar ne domin rokon ta kafa kwamiti da zai gano wurin da dokar jihar ta samu rauni da har wasu 'yan ta'adda ke cin karensu babu babbaka a jihar. Amira ta bayar da shawarar cewa ya kamata majalisar ta daukin gaggawa da zarar ta gano inda dokar ke da rauni domin kawo karshen matsalar baki daya. Shugabar ta ce kamata ya yi dokar kashe masu garkuwa da mutane da gwamna Ganduje ya kirkira ta hada da masu satar yaran. Kuma ta ce, "Muna kira ga majalisa a kan ta kirkiri wata doka za ta tilasta gwamnatin jiha ta bawa hukumomin tsaro dukkan goyon baya da tallafin da suke bukata domin gano ragowar yaran da aka sace da kuma dawo da su hannun iyayensu." Ban da wannan, Amira ta furta cewa, "Ya kamata majalisa ta yi dokar ake kulle duk wani gida da aka samu ana amfani da shi wajen boye mutanen da aka yi garkuwa da su, sannan kuma a tuhumi mai gidan. Sannan muna kira ga wannan majalisa a kan ta umarci gwamnatin jihar Kano ta janye wakilcin da 'yan kabilar Igbo da kungiyar Kiristoci (CAN) ke da shi a gwamnatin jihar saboda ba mu ga wata fa'idar shigo da su cikin harkokin da suka shafi jihar Kano kawai ba." Da yake mayar martani ga wakilan kungiyoyin matan, shugaban majalisar jihar Kano, Alhaji Abdulazeez Garba Gafasa, ya yaba wa matan a kan matakin da suka dauka na zuwa majalisar domin gabatar da korafinsu. Masu sauraro, yanzu ga wani labarin da ya shafi shirin noma da gwamnatin Najeriya ta tsara don mata. Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa, ta kaddamar da shirin kara jawo mata a cikin harkokin noma ta yadda za su rika samun tallafi da karfi daidai da maza. Furucin hakan ya fito ne daga bakin Ministan noma Sabo Nanono a lokacin da yake yin jawabi a wurin kaddamar da shirina Abuja, inda Nanono ya kara da cewa, manufa da muradin shirin shi ne a bayar da dama daidai ga kowane jinsi na maza da mata domin a bunkasa samar da abinci a Nijeriya. Nanono ya sanar da cewa, mata su ne kashi hamsin a cikin dari na yawan al'ummar duniya, inda ya ci gaba da cewa, kashi saba'in a cikin dari masu ayyukan noma a yankunan karkara. A cewar ministan, har ila yau matan su ne ke da kashi sittin a cikin dari na yawan masu ayyukan sussuka da gyaran amfanin gona, inda ya yi nuni da cewa, amma duk da haka ba su da tattalin arzikin kayan amfanin gona a hannun su. Ministan ya ci gaba da cewa, kayan amfanin gona da mata ke mallaka bai fi kashi ashirin a cikin dari ba, inda ya ce, wannan babbar matsala ce. Nanono ya kuma koka dangane da karancin ilmin mata da kuma rashin yawaitar mata a fannonin bincike, inda ya yi kira ga mata da su tashi tsaye, su daina nuna kasala ko jan-kafa, su rungumi fannonin noma don a rika damawa da su.
Yanzu ga wani labari dangane da bai wa mata damar shiga makarar horar da jami'an 'yan sanda a Najeriya.
Mai Martaba Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci jama'a da su tabbatar da ganin suna tura 'ya'ya mata zuwa Makarantar Horar da Jami'an 'Yan Sanda mata da ke Shanono, domin kokarin samun kwararrun Ma'aikatan tsaro mata. Sarkin ya yi wannan kira ne a lokacin da Shugabar Makarantar DSP Binta Muhammad, ta ziyarce shi a fadarsa a 'yan kwanakin baya. Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi alkawarin bin sawun mahaifinsa wajen bayar da gudunmawa ga cigaban wadannan Makarantu na Horar da 'Yan Sanda. Haka zalika, ya kara da cewa, "za mu bayar da dukkanin goyon bayan da ake bukata, domin daga darajar ilimi a wannan yanki." Da take magana a lokacin ziyarar Kwamandar Makarantar, DSP Binta Muhammad, ta bukaci taimakon Sarkin wajen yin kira ga al'umma, domin shigar da 'ya'yansu mata wannan makaranta, ta ce tuni aka fara yin rajistar sabbin dalibai. "Makarantun Horar da 'Yan Sanda, na koyar da darussa daban-daban, wadanda suka hada da ilimin Kimiyya da Fasaha kamar dai sauran Makarantun Sakandare, don haka, ba wai kawai an samar da wannan makaranta ba ne domin 'Yan Sanda kadai ba", in ji Binta. A cewar tata, makarantar zuwa yanzu ta yaye dalibai a bangarori daban-daban wadanda suka hada da Likitoci, Lauyoyi, Malaman Jami'a da sauran su. A wani cigaban kuma Sarkin na Bichi ya jaddada goyon bayansa ga kungiyar dalibai da ke koyon ilimin Kimiyya da Fasaha na reshen Jami'ar Bayero da ke Jihar Kano da kuma kungiyar daliban makarantar koyon harkokin Shari'a ta Malam Aminu Kano, da kuma kungiyar daliban makarantar koyon aikin noma ta Audu Bako da ke Danbatta domin habaka harkokin ilimi. Haka zalika, Sarkin ya bukaci daliban da su kara jajircewa wajen daga darajar ilimin harkokin lafiya, sannan ya bukace su da su kara himmatuwa a bangaren harkokin noma domin ciyar da kasar nan abinci.
A bangaren daliban da ke nazarin harkokin Kimiyya, Shugaban kungiyar daliban Abdulrahaman Musa, cewa ya yi sun je Fadar Sarkin ne domin bayyana masa aikace-aikacen kungiyar, wanda suka hada da taimakawa marasa lafiya. (Kande Gao)