logo

HAUSA

An bude bikin baje kolin CIIE na bana a Shanghai

2019-11-07 14:11:24 CRI

A yau Talata 5 ga watan Nuwanban shekarar 2019 ne, aka bude bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigo da su cikin kasar Sin karo na biyu a birnin Shanghai.

An bude bikin baje kolin CIIE na bana a Shanghai

A jawabin da ya gabatar yayin bude bikin, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bude kasuwarta ga ketare,matakin da zai ingiza bunkasar tattalin arzikin kasar da ma na duniya baki daya

Bayanai na nuna cewa, kamfanoni sama da dubu 3 daga kasashe da yankuna sama da 150 ne suka halarci bikin baje kolin na bana, daga cikinsu akwai kamfanonin kasashen waje fiye da dubu 1 wadanda suka halarci bikin na farko.

An bude bikin baje kolin CIIE na bana a Shanghai

Idan aka kwatanta da bikin na bara, a bana, fadin yankunan nune-nune da adadin kayayyakin da za a nuna, da kuma yawan kamfanonin da za su halarci biki, dukkansu sun karu. Bana fadin yankunan nune-nune, ya karu zuwa murabba'in mita dubu 300 daga murabba'in mita dubu 270 na shekarar 2018. Sa'an nan, a fannin karfin kamfanonin da suka halarci bikin a shekarar 2018, kamfanoni 220 dake cikin jerin manyan kamfanonin kasa da kasa guda dari 5 ne, suka halarci bikin, amma bana, adadin ya karu zuwa 250. Bugu da kari, bisa hasashen da aka yi, adadin sabbin kayayyaki da fasahohin da za a nuna a biki na bana, zai wuce na bikin farko.

Bikin baje koli na CIIE ya zama wata alama dake bayyana yadda Sin take gudanar da manufar bude kofa ga ketare, ya kuma nunawa duniya niyyar kasar Sin na nacewa ga manufar kasancewar bangarori daban-daban da ingiza ciniki maras shinge. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)