Hira da wasu matasan Najeriya biyu wadanda suka halarci taron matasan Sin da Afirka
2019-11-06 08:46:33 CRI
A kwanakin baya ne, aka kaddamar da taron matasan Afirka da kasar Sin a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Taron matasan, taro ne dake gudana duk shekara, domin sada zumunta da kara fahimtar juna tsakanin matasan Afrika da Sin, wanda kuma daya ne daga cikin bangarorin hadin-gwiwa karkashin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC a takaice. Manufar taron ita ce, kyautatawa da raya dangantakar bangarorin biyu. Taron na kwanaki 10 na bana, ya samu halartar matasan Afirka kimanin 95 daga kasashen nahiyar 51 da kuma Tarayyar Afrika ko kuma AU a takaice. Matasan Afrika da suka halarci taron na bana, sun ziyarci birnin Beijing da wasu biranen lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, ciki har da Guangzhou, da Qingyuan da kuma Shenzhen, inda suka kara fahimtar nagartattun al'adun kasar, da ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin kimiyya da fasaha, da kyautatuwar zaman rayuwar al'umma gami da yadda harkokin siyasa da tattalin arziki ke gudana a kasar ta Sin. Daga cikin matasan da suka zo kasar Sin don halartar taron matasan Sin da Afirka na bana, akwai wasu 'yan Najeriya guda biyu, wato malam Olukonga Olasunkanmi, ma'aikaci ne dake aiki a ma'aikatar harkokin wajen Najeriya, gami da Eromosele Ehigie Daniel, mataimaki ne na musammam ga shugaban jam'iyyar APC mai mulkin kasar. Olukonga Olasunkanmi ya ce, ya zo kasar Sin ne a matsayin daya daga cikin wakilan Nijeriya a taron matasan Sin da Afrika karo na 4, wannan wani shirin ne karkashin dandalin FOCAC. Kuma makasudin wannan taron shi ne hada matasan Sin da Afrika ta yadda za su fahimci juna su yi musayar ra'ayoyi da yin mu'amala da hada hannu kan yadda za a raya dangantakar bangarorin biyu. A ganisa, wannan taron yana da muhimmanci da kyakkyawa makoma ga dukkan bangarorin biyu. Olukonga ya ce, ya san kasar Sin tun kafin ya zo, ya kuma yi karance-karance a kanta, ya ce ya san kasar Sin tana da karfin tattalin arziki, kuma cikin shekarun da suka gabata, kasar Sin tana taka rawar gani a duniya, idan ana batun kere-kere da cinikayya da tallafin raya kasa, don haka, ya zo ne kawai don ganewa idanunsa abun da kasar ke da shi da kuma abun da take yi da take so ta nunawa duniya. Mitsa Olukonga ya ce a ziyararsa kasar Sin a wannan karo, ya ga nasarorin da Sin ta samu, musammam a fannin fasaha. Ya ce ya ziyarci kauyuka daban-daban dake kudancin kasar Sin wadanda suka samu ci gaba cikin sauri. Kuma abun da ya fi daukar hankalinsa shi ne yadda kauyen da babu mutane da yawa ke da fasahar sadarwar 5G. wanda abu ne da ya ban mamaki, saboda a wasu kasashe masu tasowa, kamar na Afrika, akwai wuraren da ba su da sadarwar 4G. Gaskiya abun ya burge shi, kasar Sin ta ci gaba sosai a fannin fasaha. Game da ci gaban da kasar Sin ta samu a sauran wasu fannoni kuma, Olukonga ya ce, ba a fannin fasaha kadai ya tsaya ba, inda ya ce, cikin lokacin da ya shude, kasashen Afrika ne suka fi cin gajiyarta, kuma wannan tallafin na zuwa ne ta sigogi daban daban, kamar bada rance da zuba jari a fannin ginin ababen more rayuwa da kudin horar da jami'an gwamnatoci. Ya ce ya san cewa gwamnatin kasar Sin na daukar nauyin horar da jami'an kasashe masu tasowa wajen kawo su nan da ba su horo a kai a kai, dukkan wadannan shirye-shirye ne suka sa kasar Sin ta zama zakaran gwajin dafi. Da ya tabo magana kan babban dalilin da ya sa kasar Sin ta samu irin wannan ci gaba, Olukonga ya ce, abun da ya sa kasar Sin ta fita daban ko ta samu ci gaba shi ne, shugabanci na gari kuma mai karfi. Ya ce, a cudanyar da ya yi da matasan kasar Sin, ya gane suna girmama shugabansu, wato shugaba Xi Jinping, kuma irin shugabancin da yake yi, la'akari da yawan al'ummar kasar, da karfafa musu gwiwar tunkarar kalubalen da ba a saba gani ba, ya ingiza su zuwa wannan mataki da suke a yanzu. Haka kuma, kasar Sin ta zuba kudi sosai a fannin samar da ilimi, kuma abu ne da kowa ya sani cewa, ci gaba na tafiya ne kafada da kafada da ilimi mai inganci, kuma a ganisa kasar Sin ta yi namijin kokari a wannan fannin, ta yadda suka kai ga tabbatar da matasan kasar suna da abun yi, kuma wannan ya taimaka ga gagarumar ci gaban da kasar ta samu.
Shi ma a nasa bangaren, mataimaki na musammam ga shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Mista Eromosele Ehigie Daniel ya bayyana ra'ayinsa game da halartar taron matasan Sin da Afirka a kasar Sin, inda ya ce, da farko sun yada zango ne a fadar mulkin kasar Sin wato Beijing, inda aka bude taron. Sannan an yi musu bayani game da makasudin taro, wanda ke da nufin karfafa dangantakar Sin da kasashen Afrika. Kuma ya ce kwalliya ta biya kudin sabulu saboda ya kara fahimtar dangantakar Sin da Afrika. Sun ziyarci wurare masu ban sha'awa da dama. Kuma ya ce sun koyi abubuwa da dama a cikin kwanaki kalilan, inda yake matukar farin ciki.
Mista Eromosele Ehigie Daniel ya ce, a ziyarar da ya yi a kasar Sin, ya gano akwai kamanceceniya tsakanin kasarsa Najeriya da kasar Sin. Ya ce, bayan bude taron a rana ta farko, sun ziyarci wuraren al'adu, inda aka nuna musu wasu kayayyakin kidekide, kamar jita da ganguna kamar dai irin na gida. Har ma ya buga ganga, saboda a gida Afrika ma suna amfani da ganga. Da ya gan shi ba wani sabon abu ba ne, kuma bai yi tsammanin Sinawa na da irin wannan al'ada ba, gaskiya wannan na daya daga cikin kamanceceniyar da ya gani tsakanin bangarorin biyu. Da ya bayyana ra'ayinsa kan babban dalilin da ya sa kasar Sin ta samu babban ci gaba da dimbin nasarori, Mista Eromosele Ehigie Daniel ya ce, k;asar Sin ba sabuwar kasa ba ce, kasa ce da ta ci gaba, inda ya ce ba zai yi mamakin irin ci gaban da ta samu ba. Ko a gida Najeriya, sun yi karatu akan kasar Sin da ma Asiya baki daya, kasar Sin kasa ce da kowa ya sani a Nijeriya, don haka ganin ci gaban da ta samu ba abun mamaki ba ne. Amma abun da ya fi ba shi sha'awa shi ne, yadda suka tabbatar da dorewar ci gaban da suka samu. Da ya tabo magana kan wuraren da kasar Sin ta yiwa kasashen Afirka zarra, Eromosele Ehigie Daniel ya bayyana ra'ayinsa cewa, ba ya jin idan aka kwatanta kasashen Afirka da kasar Sin sun yi kansu adalci. Saboda wadannan kasashen biyu na da bambamci. Da farko sai da aka yi mulkin soji a Nijeriya, kuma duk inda aka yi irin wannan mulki za a samu keta dokoki. Yanzu an fara demokradiyya, suna kokarin saita alkiblar Nijeriya. Ya ce ya yi amana, nan bada dadewa ba, Nijeriya za ta kai matakin da kasar Sin ta kai. Bana kasar Sin ta cika shekara saba'in da kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar, kuma a wadannan shekaru, kasar ta samu babban ci gaba da dimbin nasarori a karkashin tsarin gurguzu mai salon musamman irin na kasar. Game da wannan batu, Eromosele Ehigie Daniel ya ce, idan kana bin wani tsari, kuma kana jin dadinsa, to sai ka ci gaba da binsa. Ya ce yana ganin Sinawa suna farin ciki da yadda ake tafiyar da gwamnati. Ya yi misali da wani gari da suka je, wanda aka ce musu a da karkara ce, abun da ya gani a can ya ban sha'awa. Wato abun da ya fi muhimmanci a tsarin gwamnati shi ne, ayyukan da gwamnati ta aiwatar, don gaskiya abun da ya gani ya burge shi kwarai, don kauyen ya zama maraya sosai. Bisa hikima da hangen nesa irin na shugaban kasar, ya ja hankalin kamfanoni zuwa yankin, inda su kuma suka dauki 'yan asalin wuri aiki, sannan ake samar da kayayyaki a wajen. Baya ga haka, an samar musu da sadarwar intanet, inda suke amfani da ita wajen tallata kayansu akan intanet. Wannan shi ne abun da mutane suke bukata, ai gwamnati ta mutane ce, idan har kana hidimta musu, to ka gama komai.
A karshe, yayin da yake tsokaci kan dangantakar dake kasancewa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, Eromosele Ehigie Daniel ya ce, ana samun kyautatuwar alakar. Ya ce, daga abun da ya ji, wannan taron shi ne karo na 4, an yi na 1 da na 2 da na 3, don haka a wannan lokaci, dole a ce akwai hadin gwiwa tsakanin bangarorirn 2. Kuma daga abun da ya gani, akwai wata irin kyakkyawar alaka tsakanin bangarorin Sin da kasashen Afrika. Tabbas shugaban kasar Sin Xi Jinping yana da hangaen nesa da kaifin basira, la'akari da yadda yake iya hango abubuwa masu amfani kuma yake aiwatar da su, ko da kuwa a lokacin ba za a ga ribar hakan ba. Ya ce ya san cewa da irin kudin da ake kashewa, ya tabbata shugaban kasar ya ga wani abu mai amfani da zai auku a nan gaba idan aka kyautata dangantakar.(Murtala Zhang)